HIMMA DAI MATA MANOMA: Takin zamani ba shi da amfani idan bai magance tsadar abinci ko ya kara yawan kayan gona ba – Manomiya

0

Agrihub Nigeria cibiya ce ta horas da dabarun noma, kuma katafariyar gonar harkokin noma ce da ke noma dankalin Turawa mai tarin yawa, a Jihar Ogun.

Wata mata ce mai suna Aderonke Eko-Aderinde ta kirkiro tare da kafa Agrihub Nigera, kuma ta zanta da PREMIUM TIMES inda ta fede biri har wutsiyar yadda ta fara harkar noma har zuwa bayanin yadda ko halin da harkokin noma ke ciki ko aka tsoma shi a ciki, kamar yadda za a ji daga gare ta.

“Yadda na tsinci kai na a harkokin noma abu ne da zai ba mutane mamaki kwarai. A ce dai ni da aka haifa a cikin Lagos kuma na tashi a Lagos, a ji yadda na tsunduma harkar noma, za a yi mamaki sosai.

“A unguwar Surulere na tashi, kuma a can na yi firamare da sakandare. A Yaba na yi jami’a. Kun ga ni cikakkar ‘yar Legas ce kenan.

“Na kasance ina shawa’ar noma tun ina jami’a, kuma ban cika shekaru 20 a duniya ba hankali na ya koma ga noma. A ajin mu babu mutum daya mai sha’awar noma.Hatta malamin da ya rika koyar da mu dabarun noma, bai ba ni shawarar na tsunduma harkar noma ba. Ce min ya yi na nemi wani abin daban. Saboda haka da zan fara, sai ya kasance ba ni da wani abokin shawara na musa, sai dai na rika bazama ina tambayoyi da bincike.

“Lokacin bautar kasa (NYSC), an tura ni Arewa, inda a can ne na fara goyayya da cudanya da tantagaryar manoman karkara.” Inji ta.

Ta ci gaba da cewa ta na kammala bautar kasa, sai ta fara jaraba harkar noma a garin Epe.

“To dan noman da na fara a Epe sai na fahimci masu karamin karfi a harkar noma wahala kawai su ke yi. Daga nan na fara tunanin yadda zan samu jarin da zai habbaka min harkokin noma na. Sai na fara dinki, kuma na rika neman kwangilar dinki mai yawa.

“Na taki sa’a wani kamfani ya ba ni kwangila, kuma aka biya ni kudi mai kauri. To daga nan na fara karfafa sana’ar noman da na fara a lokacin.”

Ta ce abin da ya Bankin Manoma (BOA) ba shi da wani tasiri a harkar noma wajen bunkasa shi, saboda tun asali ba a gina masa ginshikin harkar noma wanda zai tasiri wajen bunkasa harkokin noma ba.

Ta ce matsawar masu kula da wani muhimmin abin ci gaban jama’a ba su da kishi ko kwarewa akan abin da ake so a bunkasa din, to babu yadda za a samu nasara.

An tambaye ta batun tasirin takin zamani, sai ta ce ya kamata zuwa yanzu a daina kafa hujja da cewa idan aka wadata manoma da takin zamani, wai shikenan an magance gagsimar matsalar da ke addabar harkar noma.

“Maganar idan aka wadata manoma da takin zamani wai an magance matsalar da manoma ke fuskata, wannan kwata-kwata ba gaskiya bace.

“Takin zamanin nan dai ko an wadata manoma da shi, ba ya magance matsalar tsadar kayan abinci. Wadatar takin zamani ba ta rage farashin kayan abinci. Kuma idan ka lafta takin zamani a gonar ka, amfanin gonar da za ka noma ba kara yawa zai yi ba. Idan ka ga kayan gonar da ka noma sun kara yawa, to kara wa ginar ka fili ka yi, amma ba saboda takin zamani ba.

“Sannan kuma shi takin zamanin nan, ba kala daya ne tal ake amfani da shi kan kowace shuka ko kayan gona ba. Saboda haka, takin zamani ba shi da wani tasirin da ya ke iya magance matsalar da manoma ke fuskanta. Ina ganin ma ba shi cikin lissafin matsalolin manoma.” Cewar ta.

Share.

game da Author