Masarautar Bauchi ta dakatar da Wakilin Birnin Bauchi saboda ya kece Sarki a adon Sallah

0

A wata takarda da ta fito kai tsaye daga masarautar Bauchi, ta bayyana cewa masarautar ta dakatar da Wakilin Birnin Bauchi, Dan majalisa, Yakubu Shehu Abdullahi, saboda ya yi adon da ya kece sarki a ranar hawan Bariki a Bauchi.

A al’adar Hausa, ba a adon da ya kece sarki a ranar hawa ko kuma ado daidai da na sarki, sai dai a yi kasa da adon sarki.

Shiko Honarabul Yakubu yayi ado ne kamar wani sarki san ye da Alkyabba ba azo agani da kuma Kandiri, irin wanda kasaitattun sarakuna ke saka wa.

Majalisar sarkin Bauchi ta bayyana cewa tun kafin a fito hawa an bishi har gida an gargade shi da kada ya kuskura ya yi irin wannan shiga amma ya ki ji.

” Abinda ya faru a gidan gwamnati ya nuna ka raina sarki, masarauta, gwamna da gwamnatin jihar, kuma majalisa ba za ta yarda da wannan ba. Saboda haka ta dakatar da kai daga sarautar Wakilin Birnin Bauchi har sai abin da hali yayi.

An ce ko a lokacin da ya kawo jafi wa sarkin Bauchi, Honarabul Yakubu bai waiwayi gwamnan jihar ba dake zaune musa da sarmi don ya gaishe shi ba.

A karshe dai majalisar sarkin ta ce sai da ta yi nazari mai zurfin gaske kafin ta yanke wannan hukunci.

Share.

game da Author