Sarkin Kano Mai Murabus, kuma Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya bayyana cewa tulin basussukan da Najeriya ta ciwo a kasashen waje idan aka kwatanta da 2011 zuwa 2021, to ya rubanya yawan kudin shigar da Najeriya ta samu sau 400.
Sanusi, wanda shi ne Sarkin Kano mai murabus, ya nuna tsananin damuwa kan irin gudun famfalakin ciwo bashin da Najeriya ke yi, wanda ya ce abin ya yi munin da zai iya jefa kasar a cikin ramin da samun wanda zai iya ceto ta, sai an sha wahalar sosai.
A ranar Alhamis ce Sanusi ya nuna wannan damuwar a wani taron-taron-daga-gida na ‘onlline’, da aka shirya kan matsalar da tattalin arzikin Najeriya ta shiga, da yake batun nema da rokon a yafe wa kasar wasu basussukan da su ka hana tattalin arzikin kasar farfadowa.
Gidauniyar Heinrich Böll Foundation ce ta shirya taron, inda a karin hasken da Sanusi ya yi, ya kara da cewa ana ta maganar cewa Najeriya na da karfin arzikin biyan bashi, amma an manta da wani muhimmin abu dangane da matsala ta biyan bashi.
“Idan ka shiga ka yi nazarin rahoton da mujallar Babban Bankin Najeriya (CBN) ya wallafa cikin 2011, za ka ga cewa gwamnatin tarayya ta samu kudaden shiga daga kowane bangarorin karbar harajin ta na tarayya, har tsabar kudi naira tiriliyan 18.9 a kan dala 1 na adadin naira 165. Wato kenan kudin shigar da gwamnatin tarayya ta tara a 2011 ya kai dala biliyan 55.5 a kan dala 1 naira 165.
“To amma bashi a lokacin bai wuce dala biliyan 5 ba. Sai dai zuwa shekarar 2020 bashin kasashen waje ya kai dala biliyan 33.4, sannan kuma kudin shiga bai wuce dala biliyan 8.3 ba.
“Kenan tulin bashi a ma’aunin kudaden shiga ya tashi daga kashi 8% bisa 100%, ya koma kashi 400% bisa tsakanin 2011 da 2020.
“Wannan kuwa wani gagarimar guguwar matsalar tattalin arziki ce wadda idan ta tirnike nan gaba, ba a san yadda za a iya kwantar da ita ba.
“Abin takaici kuma har yau Najeriya da kudaden fetur ta dogara wajen samun kudaden shiga. An kasa fadada tunanin kirkiro hanyoin da kasar za ta rika samun kudaden shiga baya ga danyen man fetur.”
Sanusi ya yi wannan bayani dalla-dalla na matsalar da ta dabaibaye Najeriya kan kudaden bashin da ake bin kasar, kuma ake ci gaba da falfala gudun famfalakin ciwowa. Sannan kuma a gefe daya ga matsalar karancin kudaden shiga da ake fama da su daga danyen man fetur din da ake takama da shi.
TSARIN CIWO BASHI DA BIYAN BASHI: Wankin Babban Bargon Da Sanusi Ya Yi Wa Gwamnatin Buhari:
Sanusi ya yi nazarin cewa irinyadda Najeriya ke auna karfin iya biyan bashin da ta ke ciwowa a kan ma’aunin karfin arzikin kayan cikin gida wato GDP, ko ‘Gross Domestic Product’, to wannan ma’aunin har gara kwanon awon barkono ko zoborodo da shi.
“Ai ba a rika biyan bashi da kudaden GDP. Sai dai ka rika biyan bashi da kudaden shigar da kasa ke samu.” Inji Sanusi.
“Yanzu misali, idan ka na kwasar kashi 20 kadai na kudaden GDP ka n aka na biyan bashi, to zai iya kasancewa ka na yi wa bisyan bashi hidima da kashi 100 na kudaden shiga kenan.
Ya kuma nuna yadda Chana ta shige gaba wajen dirka wa Najeriya basussukan da aka karba tsakanin kasa da kasa, har aka karbi dala bilyan 3.2 daga Chana, wato kashi 78% na bashin dala biliyan 4 da aka karbo.
Kan haka ne Sanusi ya ce yanzu Chana ta zame wa Najeriya karfen-kafa, ta yadda babu yadda kasar nan za ta yi zaman tattauna batun bashi, ba tare da Chana na wurin ba.
Sanusi ya ce kiraye kirayen a yafe wa Najeriya basussukan da za a iya kauda kai, abu ne mai kyau, amma fa tilas hakan ba za ya yiwu ba, har sai kasar nan ta nuna cewa da gaske ta ke yi, ta yi gyara kan matakai da tsare-tsaren inganta tattalin arzikinta tukunna.
“Akwai fa’ida idan aka yafe wasu basussukan, to amma fa sai an ga yadda Najeriya ta yi gyara wajen tsare-tsaren tattalin arzikin ta tukunna.
Bai yiwuwa ka ce ka na biyan kusan kashi 90 na kudaden shigar kasa ga biyan bashi, sannan kasa ta yi tunanin za ta ya ci gaba ko za ta iya fita daga halin kaka0-ni-ka-yin da ta shiga. Ya ce ai an tashi tsaye haikan wajen ginawa da zuba jari a bangaren ilmi, gona da irin su kiwon lalfiya.
“Sannan wasu wasu sassan kasar nan da yawan hayayyafan da ake yi ya rinjayi karfin tattalin arzikin jama’a. Za ka iya samun akalla a ce yawancin gidaje ana haihuwar yara kakwai zuwa 8.”
Ya ce duk kasar da ke cikinirin wannan yanayi, kuma tattalin arzikin ta ba karuwa ya ke yi ba, za a dade ana cikin garari.