Zargi: Wani rahoton da ke daukar hankali yanzu na bayyana cewa akwai wata sabuwar allurar rigakafin da ke kare mutum daga kamuwa da cutar Kanjamau, wadda tun a gwajin farko ta ke nuna cewa tana da karfin kashi 97 cikin 100 wajen inganta garkuwar jikin mutum.
Cutar HIV cuta ce da ke karya garkuwar jikin dan adam musamman kwayoyin jini, wadanda a turance ake kiransu CD4 cells. Da zarar kwayar cutar HIV ta shiga jikin dan adam, ta kan fara da kashe wadannan kwayoyi na CD4 cells din ne ta yadda garkuwar jiki za ta raunata. Idan har haka ya faru, jikin ba zai iya yaki da cututtuka ba musmman irinsu tarin faku da ma wasu nau’o’in cutar daji.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, daga karshen shekara ta 2019 mutane miliyan 38 ne ke rayuwa da cutar HIV a duniya.
WHO ta ba da shawarar cewa duk wani wanda watakila na da hadarin kamuwa da cutar ya je ya yi gwaji. Kuma duk wanda aka gano yana dauke da cutar, a ba shi, ko kuma a yi mi shi hanyar samun maganin bayan an yi gwaji. Wadannan magunguna, idan har a ka yi amfani da su bisa ka’ida za’a rage yaduwar cutar.
Ana iya gano cutar idan aka yi amfani da na’urorin gwajin da ke ba da sakamako nan take, wadanda basu da tsada kuma suna da saukin sha’ani. Sai dai yana da kyau a ce wuraren da ke yin gwajin sun bi wadansu ka’idoji biyar masu mahimmanci wadanda za su taimaka wajen yin gwajin.
Na farko dai dole a sami amincewar wanda ya zo yin gwajin a hukumance cewa ya yarda a yi gwajin ba tilasta masa aka yi ba. Na biyu, duk me sakamakon ya gwada ya kasance sirri ba wanda ya kamata ya sani. Na uku a tattauna da duk wanda ya zo gwajin a kuma amsa tambayoyin shi. Na hudu a fadi gaskiyar abin da sakamakon ya nuna banda rufa-rufa. Daga karshe a hada shi da wurin da zai sami magani ko kuma dai duk wani abun da yake bukata bayan gwajin.
Ba da dade wa bane hoton wani rahoto mai dauke da wannan bayani ya bayyana yana mai cewa:
“Wow! An sami sabuwar allurar rigakafin HIV mai karfin kashi 97 cikin 100 wajen kare garkuwar jikin dana dam, tun a matakin farko na gwaji. Kawo yanzu, wannan ne sakamako mafi tasiri a tarihin gwajin allurar rigakafi. An yi amfani da wasu daga cikin sinadaran allurar rigakafin COVID-19 na kamfanin Mordena ne, kuma babu shakka cigaban da ake samu daga fasahohin da ake amfani su wajen dakile cutar COVID-19 zasu sauya magungunan cutar daji da HIV nan gaba.”
Tantancewa
DUBAWA ta fara da binciken kalaman da aka yi amfani da su wajen rubuta wannan labarin. Daga nan ne ta gano rahoton labarin na ainahi wanda aka wallafa a shafin wata mujallar kamfanonin magungunan Turai. Rahoton ya ce wani sabon mataki da aka dauka wajen kirkiro sabuwar allurar rigakafin da zata kare mutane daga kamuwa da cutar HIV na nuna alamun nasara tun a matakin farko na gwaji.
Bisa bayanan da cibiyoyin bincike da samar da allurar rigakafin HIV na IAVI da Scripps Research suka bayar, allurar ta taimaka wajen kirkiro irin kwayoyin da ba kasafai ake samunsu ba, kuma wadanda ake bukata wajen inganta garkuwar jikin mutun. An sami wannan nasara a kashi 97 cikin 100 na wadanda suka amince a yi gwajin allurar a kansu.
Allurar ta iya ta tantance kwayoyin jikin da ake bukata, kuma wannan na iya kasancewa matakin farko na dabarar amfani da matakai daban-daban na samar da allurar rigakafin da za ta yaki cutar HIV da ma wasu cututtukan.
DUBAWA ta kuma sake gano wata sanarwar ‘yan jarida da IAVI, da Scripps Research suka fitar ranar uku ga watan Fabrairun 2021 suna sanar da wannan labari da ma gwaje-gwajen da suke wa allurar da suka kira IAVI G001 bayanda suka gaza cimma nasara da Uhambo.
William Schief wani farfesa mai nazarin garkuwar jikin dan adam a Scripps Research kuma shugaban sashen kirkiro allurar rigakafi a IAVI wanda kuma a dakin gwaje-gwajen shi aka kirkiro allurar ne ya sanar da wannan sakamakon. Ya kuma kara da cewa wannan hanya ce da ke nuna cewa ana iya kirkiro allurar rigakafi wa cutar HIV.
“Wannan binciken ya bayar da hujjar cewa akwai ka’idojin samar da sabon allurar rigakafi na HIV wanda ma za a iya amfani da shi a wasu cututtuka na daban. Mun yi imanin cewa wannan mataki zai taimaka wajen kirkiro da allurar rigakafin HIV da ma wasu cututtukan da ake fama da su.” … kadan daga cikin bayanin Schief
Sanarwar ta kuma baiyana cewa IAVI da Scripps Research za su hada gwiwa da kamfanin Moderna dan yin gwaje-gwaje kan allurar, dan kirkiro ingantattun kwayoyin da zasu taimaka wajen hanzarta yunkurin samar da allurar rigakafin HIV.
A wani bidiyon Youtube. IAVI ya yi bayani kan gwajin da suka yi da ma irin abubuwan da suka koya wajen yin allurar.
To sai dai ya dace a jaddada cewa wannan gwajin a matakin farko ne kawai kuma akwai sauaran matakai biyu da ya kamata a bi kafin a amince da allurar rigakafi nhar ma a ba da shawarar amfani da ita.
A Karshe
Rahoton da ake ta yadawa cewa wai an kirkiro allurar rigakafin cutar Kanjamau mai karfin 97 cikin 100 wajen inganta garkuwar jiki tun a matakin farko na gwaji gaskiya ne. Sai dai wannan ne matakin farko a cikin matakai ukun da ya kamata a dauka wajen tantance allurar rigakafi. Dan haka akwai sauran matakai biyu da za’a ketara kafin a tabbatar an tantance kaifin maganin da tasirin shi a jikin dan adam
Discussion about this post