‘Yan sanda sun kashe mahara 3, sun kwato dabobbi 330 a jihar Katsina

0

Dakarun ‘yan sandan jihar Katsina sun kashe wasu mahara uku kuma ta kwato dabobbi 330 a jihar.

Kakakin rundunar Gambo Isah ya sanar da haka a zantawa da yayi na manema labarai ranar Litini.

Isah ya ce a ranar Litini ‘yan sandan sun yi arangama da maharan a Mararabar-Gurbi.

” Maharan dauke da manyan makamai sun tara dabbobi masu yawa suna kora su daga wasu kauyukan da suka sato su. Daga nan ne ‘yan sanda suka dira musu, suka fatattake su har suka kashe mahara uku sannan suka kwato dabbobin.

Ya ce an kwato babban bindiga Ak47 guda daya, shannu 160, tumaki 170 da babura biyu.

Bayan haka Isah ya ce rundunar tare da hadin guiwar kungiyar ‘yan banga sun kama Ibrahim Ma’aruf, mai shekaru 40, a kauyen Runka dake karamar hukumar Safana.

Ya ce Ma’aruf shahararre ne wajen yin garkuwa da mutane, siyar da makamai da sace-sacen dabobbi.

‘Yan sanda sun kama Ma’aruf a dalilin bayanan sirri da wasu suka sanar da yan sandan bayan ganinsa da suka yi da dabobbi 40 a Dutsen-Ma kusa da karamar hukumar Safana.

‘Yan sanda sun dade suna neman Ma’aruf ruwa a jallo domin akwai ranar da Ma’aruf ya gudu ya bara harsashin babban bindiga na Ak47 guda 96, tsabar kudi Naira 780,000 a shingen tsaron ‘yansanda dake hanyar Dutsinma zuwa Safana da ya ga ‘yan sanda za su ritsa da shi.

Share.

game da Author