A ranar Talata ne rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ceto wata yarin ya mai suna Aisha Jibrin mai shekaru 15 daga cikin wani daki da iyayenta suka kulle ta na tsawon shekara 10.
Wannan abu mai cike da mamaki ya faru ne a kwatas din Darerawa dake karamar hukumar Fagge.
Kakakin rundunar Abdullahi Kiyawa ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai a garin Kano.
Kiyawa ya ce rundunar ta samu labarin cewa iyayen Aisha, Mohammed Jibrin da Rabi Jibrin sun kulle ‘yarsu a daki tun tana da shekaru biyar da haihuwa.
Ya ce Aisha ta yi zaman wannan daki ba tare da tana samun kula ba har na tsawon shekara 10.
Kiyawa ya ce jami’an tsaro sun kai Aisha asibitin Murtala Mohammed domin likitoci su duba ta.
Ya ce mahaifiyar Aisha, Rabi na tsare a hannun ‘yan sanda sannan mahaifin Mohammed ya cika wa wandonsa iska ya gudu.
Kiyawa ya ce fannin gurfanar da masu aikata laifuka irin haka za ta ci gaba da gudanar da bincike.
Cin zarafin yara kanana abu ne da ya dade yana faruwa inda a dalilin haka kungiyoyin kare hakin rajin dan adam suka yi kira ga gwamnati da ta dauki matakin kare hakin yara kanana a kasar nan.
Jihohin kasar nan da Suka hada da Kebbi, Kaduna, Kano da sauran su na cikin jihohin da suka kafa dokar Kare hakin yara kanana.