Kafafen yada labarai sun ruwaito cewa an dakile yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, kwanaki biyu kafin rantsar da zababben shugaban kasa, Mohamed Bazoum.
Gidan Radiyo da Talbijin na FRANCE 24, ya ruwaito wakilin su Cyril Payen da ke birnin Yamai y ace sojojin da ke gadin Fadar Shugaban Kasa sun fafata da tsakar daren Talata sun a musayar wuta da sojojin da su bka yi yunkurin juyinmulki.
“An ji rugugin musayar wuta da manyan makamai da kuma kananan bindigogi a kusa da fadar shugaban kasa. Sojojin da ke gadin fadar ne su ka dakile yunkurin juyin mulkin.” Inji Payen.
“Abin da mu ka sani tabbas kwana biyu kafin a rantsar da sabon shugaban kasa, zai fuskanci matsalar tsaron da ke addabar kasar, musamman matsalar ’yan ta’adda. Amma ba mu taba tunanin yunkurin juyin mulki ba. Cewar Fadar.
Kafafen yada labarai ciki har da BBC, AFP da REUTERS, duk sun ruwaito labarin yunkurinjuyin mulkin, wanda su k ace an shafe mintina 15 zuwa 20 ana musayar wuta tun wajen karfe 3 na dare, a ranar Talata, wayewargarin Laraba.
Gidan Radiyon BBC ya tabbatar da cewa sojoji ne su ka yi yunurin juyin mulki a Nijar
“Yunkurin juyin mulki ka iya zama dalilin da ya haifar da harbe-harbe a kusa da Fadar Shugaban Kasar Nijar a daren Talata.
“Tun misalin karfe 3:00 aka fara jin harbe-harben kuma an dauki tsawon kusan minti 15 ana yi.
“Jami’an tsaron fadar shugaban kasa ne suka dakile yunkurin, wanda ya faru kasa da kwana biyu kafin rantsar da zababben shugaban kasa, Mohamed Bazoum.
BBC ta ce Sai dai gwamnati ba ta tabbatar da yunurin juyin mulkin ba ya zuwa yanzu.
Tarihin Nijar wadda ke daya daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya, cike yake da juyin mulki na soja da kuma hare-haren ‘yan bindiga masu ikirarin jihadi da ke sanadiyyar rasa rayuka.
Haka kuma an bada rahoton cewa an kama wasu sojoji a Nijar bayan yunkurin ‘juyin mulki’
Wata majiyar tsaro ta shaida wa kamfanin labarai na AFP cewa an kama wasu sojoji a Jamhuriyar Nijar biyo bayan yunkurin juyin mulkin da wasu dakaru suka yi a daren Talata.
Har yanzu babu cikakken bayani game da abin da ya faru yayin da birnin Yamai ya kasance cikin shirin ko-ta-kwana.
Tun misalin karfe 3:00 aka fara jin harbe-harben kuma an dauki tsawon kusan minti 15 ana yi.
“Jami’an tsaron fadar shugaban kasa ne suka dakile yunkurin, wanda ya faru kasa da kwana biyu kafin rantsar da zababben shugaban kasa.”
Tun bayan bayyana sakamakon zabe dai wanda ya sha kaye, Mahamed Ousmane y ace bai amince da sakamakon zaben ba, domin an yi masa magudi.
Tuni kuma ya garzaya kotu, inda ita kuma kotun kasar ta tabbatar wa Bazoum nasara a zagayen zaben na biyu.