Kungiyar Likitocin Najeriya ta shiga yajin aikin game-gari, kwana biyu bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi kasar Ingila domin ganin likitocin sa.
Kokarin da gwamnatin Tarayya ta yi domin shawo kan lamarin, ta hanyar kiran taron sasantawa da Ministan Kwadago, Chris Ngige ya yi da shugabannin kungiyar likitocin ta NARD a ranar Laraba, bai haifi da mai idanu ba, domin taron bai hana likitocin tafiya yajin aiki ba.
“Mun fara yajin aiki tun daga yau Alhamis karfe 8 na safe, yayin da a gefe daya kuma mu na nazarin tayin da gwamnatin tarayya ta yi mana”. Inji Shugaban Kungiyar Likitocin Najeriya, Uyilawa Okhuaiheuyi da a Turance a ke kiran ta da suna NARD.
Wannan furucin da ke sama, shugaban ya yi shi ne ga wakilin PREMIUM TIMES a safiyar Alhamis.
Kungiyar Likitocin Najeriya ta yi barazanar tafiya yajin aiki muddin gwamnatin tarayya ta kasa biya masu bukatun su, ciki kuwa har da biyan su hakkokin su na alawus-alawus da su ke bi ba a biya su ba.
Sun tafi yajin aikin ne a daidai lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi Ingila, domin likitocin sa a Landan su duba lafiyar sa.
Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa ba wani bakon abu ba ne don Buhari ya tsallake daga Najeriya ya tafi Ingila ganin likita.
“Buhari ya shafe shekaru 30 ya na zuwa ganin likitan sa a Landan.” Inji Kakakin Yada Labarai na Shugaba Buhari, wato Malam Garba Shehu.
Shugaban na NARD ya ce dama sun bai wa gwamnatin tarayya wa’adin a biya masu bukatu kafin ranar 31 Ga Maris ta wuce. Don haka tunda ta wuce din ba a biya masu ba, shi ya sa su kafaa yajin aiki daga ranar Alhamis, 1 Ga Afrilu, 2021.
Wadannan likitoci da ke kan amun horon zama cikakkun manyan likitoci, su ne mafiya yawa a asibitocin kasar nan.
Abubuwan Da Su Ke Bukata Daga Gwamnatin Tarayya:
Su na o a biya su kudaden albashin su na baya da ba a biya su ba. Su na bukatar a sake duba kankantar kudaden alawus din saida rai da ake biyan u. Sun nemi wannann alawus na saida rai ya kai kashi 50 bisa 100 na adadin kudin albashin kowa.
Sannan kuma su na bukatar a biya su kudaden alawus-alawus na aikin korona da su ka yi wadanda har yau bayan saida rayuka da su ka yi wajen kokarin dakile korona da kula da masu dauke da ciwon korona, har yau ba a biya su alawus din ba, musamman ma likitocin da su ke aiki a karkashin manyan asibitoci na jihohi.