Wani jirgin yakin sojojin saman Najeriya, samfurin Alpha Jet, wanda ake kai wa Boko Haram hari da shi, a Jihar Barno ya bace.
Mahukuntan sojojin sama ne su ka bayyana haka a ranar Alhamis din nan da safe.
Kakakin Hukumar Sojojin Saman Najeriya, Edward Gabkwet ya ce jirgin samfurin Alpha Jet ya bace daga idanun na’urar hangen jiragen sama, wato ‘radar’.
Air Commodore Gabwet ya kara da cewa jirgin yakin ya bace, “yayin da ya ke kai farmakin agaza wa sojojin kasa a batakashi da Boko Haram a Arewa maso Gabas.
“An daina gani ko sanin halin da jirgin yakin ke ciki, tun daga karfe 5.08 na yammacin ranar Laraba, 31 Ga Maris, 2021.”
Ya kara da cewa da zarar an ji duriyar sa, an gan shi ko kuma an san halin da ya ke ciki, to za a gaggauta sanar wa jama’a halin da ake ciki.
Bacewar jirgin yaki ta faru ne makonni kadan bayan da wani jirgin yakin samfurin Beechcraft B350i ya rikito kasa sakamakon matsalar inji da ya samu a kan hanyar sa ta zuwa Minna, Jihar Neja.
Wancan jirgin da ya fado, ya na kan hanyar sa ne ta zuwa aikin leken asiri a Jihar Neja, a wani kokarin da aka yi domin cewto dalibai da malaman sakandaren Kagara da masu garkuwa su ka rike a lokacin, a jihar Neja.
Faduwar Jirjin Yakin ta janyo asarar kananan hafsoshin soja da su ka hada da: Flight Lieutenant Haruna Gadzama (Captain), Flight Lieutenant Henry Piyo (Co-Pilot), Flying Officer Micheal Okpara (Airborne Tactical Observation System (ATOS) Specialist), Warrant Officer Bassey Etim (ATOS Specialist), Flight Sergeant Olasunkanmi Olawunmi (ATOS Specialist), Sergeant Ugochukwu Oluka (ATOS Specialist), da kuma Aircraftman Adewale Johnson (Onboard Technician).
Sojojin saman Najeriya na cikin aikin yakin da Boko Haram gadan-gadan a Arew maso Gabas da kuma yaki da harara masu yin gakuwa da mutane.
Su ne kuma ke kai hare-hare a sananonin Boko Haram a kai a kai.