Karancin maza masu bada gudunmawar maniyi don mata masu neman haihuwa ta hanyar kimiyya ya kawo cikas a kasar Sweden

0

Asibitocin dake taimakawa mata daukar ciki a kasar Sweden sun koka kan karancin maniyin namiji a asibitocin su.

Asibitocin sun ce an fara samu karancin ruwan maniyin namiji tun bayan barkewar annobar Korona.

Wata likita a asibitin Jami’ar ‘Gothenburg’ Thurin Kjellberg ta ce karancin maniyin da suke fama da shi ya kara tsawon lokacin jiran daukan ciki da matan dake bukatan su yi ciki ke yi a asibitin na su.

Kjellberg ta ce kafin bullowar Korona tsawon lokacin da macen dake bukatan daukan ciki shine watanni shida amma yanzu tsawon lokacin jira ya kai mata watanni 30.

A yanzu haka abin ya kai ga kasar Sweden na siyan maniyin namiji daga kasashen waje saboda rashin samun mazan da za su bada maniyinsu.

Dabaran amfani da kimiya wajen taimaka wa mace ta dauki kyauta ake yi a kasar Sweden sai dai idan akwai matsalolin dake hana mace daukan ciki wanda dole sai likita ya bada magani ana biyan krona 100,000 kudin Sweden ko kuma dalan Amurka 11,785.

Kjellberg ta ce yawan matan da doka ta amince a yi wa ciki da maniyin namiji a kasar ya samu cikas yanzu.

Ta ce dokar ta amince a yi amfani da maniyin namiji daya a yi wa mata shida ciki kawai a kasar.

Hakan na nufin duk namijin da ya bada maniyi sau shida ba zai kara bada maniyi ba kuma.

Bincike ya nuna cewa a kasashen Nordic da ya hada da Denmark, Finland, Faroe Islands, Iceland, Norway, Belgium da Sweden kasar Belgium ne ta fi samu yawan matan da ake amfani da kimiya domin su haihu.

Kjellberg ta ce Sweden ta yi amfani da yanar gizo domin wayar da kan maza su fito su bada maniyinsu amma bai haifar musu da mai Ido ba.

Ta ce yanzu za su yi amfani da gidajen jaridu musamman talabijin domin wayar wa maza kai.

Share.

game da Author