BAYAN TSADAR ABINCI: Malejin tsadar rayuwa ya cilla zuwa kashi 18.17% a Najeriya

0

Farashin tsadar kayan masarufi a Najeriya ya karu zuwa kashi 18.17 a cikin watan Maris, akasari duk tsadar kayan abinci ce ta haifar da shi.

Wannan bayani na kunshe cikin rahoton da Hukumar Tattara Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS) ta wallafa a ranar Alhamis, a bayanan irin yadda ‘yan Najeriya su ka tsinci kan su cikin watan Maris.

NBS dai ta na fitar da alkaluman bayanan tsadar rayuwa, hawa da saukar farashin kayan abinci da kayan masarufi a kowane wata.

NBS wacce hukumar gwamnatin tarayya ce, ta bayyana cewa farashin kayan abinci, wanda da shi ne ake auna tsadar rayuwa, ya karu da kashi 0.82 a cikin watan Maris.

Wannan tashin gwauron zabo ya zarce wanda ya yi na kashi 17.33 a cikin watan Maris.

Yayin da karin ya tabbata tsakanin watan Fabrairu zuwa Maris, PREMIUM TIMES Hausa a farkon watan Maris ta buga labarin yadda Babban Bankin Najeriya CBN ya kasa lalubo lakanin hana naira shan dukan tsiya a kasuwar tsaye a kasar nan. Kuma ya kasa gano hanyar rage wa talakawa radadin kuncin rayuwa.

Har ila yau, kwanan baya ne PREMIUM TIMES HAUSA ta buga rahoton yadda farashin kayan abinci ya shafe watanni goma ya na jijjiga aljifan talakawa.

A rahoton, an buga cewa Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO), ta bayyana cewa an shafe tsawon watanni takwas ajeri, daga watan Yuli 2020 zuwa Maris, 2021 farashin kayan abinci na tsulla tsadar tseren tsere wa karfin aljihun talakawa a fadin duniya.

Cikin wani rahoto da aka fitar a ranar Alhami, ya nuna akasarin abincin da tantagaryar taakawa su ka fi ci, ya rika yin tsadar da ya ke kokarin fin karfin talakawan.

Alkaluman kididdigar tashin farashin kayan abinci ya karu da kashi 2.1 cikin watan Maris, fiye da yadda ya ke a cikin watan Fabrairu.

Wannan karin hauhawar farashin kayanabinci kuwa, ba a taba ganin irin ta ba, tun bayan wadda aka gni cikin watan Yuni, 2014.

Rabon da man girki yay i tsadar da yay i cikin watan Maris, tun a shekarar 2011, kamar yadda sakamakon binciken da FAO ta fitar a farkon watan Afrilu din nan.

Sauran kayan abincin da FAO ta lissafa sun yi gwaron tashin farashi, sun hada har da madara da man buta, saralak,

Haka kuma farashin dawa ya fadi kasa warwas, sai kuma nama da kaji da farashin sukari, sai hauhawa su ke yi, har ta kai masu shan koko a wasu kasashe na tunanin shan sa lami salam, ba tare da zuba zukari ba.

Sai dai kuma wasu kasashen ana samun saukin farashin sukari, saboda yadda kasar Indiya ta rika dumbuza sukari zuwa kasashen duniya, domin sayarwa.

Daya daga cikin abinda ke dagula hankulan kasashe da dama shi ne tashin gwauron zabein farashin alkama, wadda da it ace ake sarrafa abinci da daman a manya da na jarirai.

Ana sa ran a duniya za a noma alkama mai tarin yawan tan milyan 785 a cikin shekarar 2021.

Yayin da wasu kasashe ke ta kokarin ganin an kauce wa matsalar tsadar rayuwa, cikin watan da ya gabata ne dai PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Bankin CBN ya rasa lakanin hana tsadar rayuwa ci gaba da yi wa talakawa kirbin-sakwarar-Ladidi.

A wancan labarin, an buga yadda taron da Kwamitin Tsare-tsare na Babban Bankin Najeriya CBN ya shirya domin labubo hanyoyin hana tsadar rayuwa tilasta wa tattalin arziki yin tsayuwar-gwamin-jaki, ya tashi ba tare da samar da wani lakanin da zai hana tsarar ta rayuwa ci gaba da yi wa talaka kirbin-sakwarar-Ladidi ba.

Masana sun yi tunanin cewa a taron manema labarai da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya kira yau Talata da rana zai shaida wa manema labarai cewa CBN zai kara kudin ruwan da bankuna da cibiyoyin hada-hada ke bai wa masu karbar ramce, lamuni da basussuuka.

To sai dai kuma a taron, Emefiele ya shaida masu cewa har yanzu adadin kudin ruwan da aka dora wa masu karbar lamuni daga bankuna na nan a kashi 11.5% bisa 100%, kamar yadda ya ke a cikin watan Fabrairu da Maris, ba a kara ba.

CBN ya nuna cewa wannan matsayi da su ka tsaya a kai, shi bankin ke ganin cewa zai iya samun karfin tura jaki ruwa, ta yadda tsadar rayuwar da aka shiga tsawon shekaru uku a jere za ta samu daidaito da farashin kayan abinci da na masarufi da kuma tattalin arziki.

Sai dai kuma a wurin taron Kwamitin, wasu sun so a dan kara adadin yawan kasafin kudin ruwan da ake dora wa masu karbar ramce a bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudade.

Share.

game da Author