LISSAFIN DAWAKAN RANO: Jihohi 36 da Abuja sun tara harajin naira tiriliyan 1.31 a shekarar 2020 –Inji NBS

0

Jihohi 36 na Najeriya idan aka hada da Babban Birnin Tarayya Abuja, sun karbi kudaden shiga na harajin naira tirilliyan 1.31 a cikin shekarar 2020.

Wannan adadi kuwa ya ragu idan aka hada da shekarar 2019, inda gaba dayan su su ka karbi harajin naira tirilian 1.33 a waccan sherarar.

Hukumar Kididdigan Alkaluman Bayanai ta Kasa, NBS ce ta fitar da wannan lissafin kudaden harajin da jihohin su ka karba, a cikin wani rahoton da NBS din ta wallafa a ranar Alhamis.

Jihar Yobe ce kutal, wadda ta fi tara mafi karancin kudaden haraji ashekarar 2020, inda ta tara naira biliyan 7.779 kacal.

Sai uma Taraba mai naira biliyan8.114, sai Adamawa mai naira biliyan 8.329, sai Gombe mai naira biliyan 8.537, Jigawa kuma naira biliyan 8.667. ita kuma Ekiti naira biliyan 8.716 kacal.

Rahoton NBS ya nuna cewa an samu nakasu, tasgaro da gibi har na -1.93% a harajin da jihohi su ka tara cikin shekarar 2020.

Rahoton y ace Jihar Lagos ce ta tara harajin kudaden shiga mafi yawa har naira biliyan 418.99. Sai Jihar Ribas mai naira biliyan 117.19. Abuja ce ta uku mai naira biliyan 92.05.

Delta N59.732 biliyan, Kaduna N50.768 biliyan, Ogun N50.749 biliyan, Oyo N38.042 biliyan, Kano N31.819 biliyan, Akwa Ibom N30.696b. Anambra N28.009b, Edo N27.184b, Ondo N24.848b sai Enugu N23.650b.

Sai kuma Osun N19.668 biliyan, Kwara N19.604 biliyan, Plateau N19.122 biliyan, Zamfara N18.499 biliyan, Kogi N17.357 biliyan, Imo N17.081 biliyan, Cross River N16.183 biliyan, Abia N14.376 biliyan, Kebbi N13.778 biliyan da Ebonyi mai N13.591 biliyan.

Benue N10.463, Niger N10.524, Katsina N11.473, Borno N11.576, Sokoto N11.796 , Bayelsa N12.180, Nasarawa N12.476, Bauchi N12.502.

Share.

game da Author