Buhari ya kara wa kamfanin dake kwangilar titin Sokoto-Tambuwal-Makera naira biliyan 8.39

0

A zaman kwamitin zartaswa ranan Laraba ne gwamnati ta kara ware Naira biliyan 8.39 domin kammala aikin titin Sokoto-Tambuwal-Jega-Makera.

Ministan aiyuka da gidaje Babatunde Fashola ya sanar da haka bayan an kammala zaman kwamitin zartaswa wanda ake yi duk Laraba a fadar gwamnati.

Fashola ya ce shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince a kara wa kamfanin ‘CRCC Construction Company’ saboda kukan hauhawar farasbin kayan aiki a fasuwa, sannan kuma da sauya fasalin aikin daga gyara zuwa a shimfina titi sabuwa shar.

Ya ce zuwa yanzu kamfanin ya kammala gina kashin farko na hanyar dake da tsawon kilomita 296 kuma kamfanin ya kammala kashi na biyu na hanyar mai nisan kilomita 100.

Abin da ya rage shine kilomita 85 na hanyar wanda ya taso daga Yauri zuwa Makera.

Wannan hanya na daga cikin manyan hanyoyin da gwamnatin Buhari ke yi a yankin Arewa.

Share.

game da Author