‘Yan sanda sun kwato awaki, babura da bindigogi daga hannun mahara a Katsina

0

‘Yan sandan da ke karkashin rundunar ‘Operation Puff Adder’ a jihar Katsina sun yi nasarar kwato awaki da babura daga hannun mahara a wani arangama da suka yi a Batsari, jihar Katsina.

Kakakin rundunar Gambo Isah ya sanar da haka wa manema a garin Katsina ranar Laraba.

Isah ya ce harsashin bindigan AK47 guda 30, awaki 24, tumaki 29 da baburan hawa 7 na daga cikin abubuwan da jami’an tsaro suka kwato daga hannun maharan.

“A ranar 20 ga Afrilu da misalin karfe 6 na safe ‘yan sandan dake karamar hukumar Batsari da rundunar Operation Sharan Daji sun tare wasu mahara a kauyen Shekewa.

“An yi batakashi tsakanin mahara da jami’an tsaro inda da dama daga cikin maharan suka tsira da raunin harsashi a jikinsu.

Isah ya yi kira ga mutane da su ci gaba da hada hannu da jami’an tsaro domin ganin an kawo karsben matsalar rashin taro a jihar.

Share.

game da Author