Da yake bayyana aiyukan da kwamitin dakile yaduwar cutar korona ta yi a jihar Gombe a shekarar 2020, shugaban kwamitin kuma mataimakin gwamna Manasseh Jatau ya bayyana cewa mutum 44 wanda a ciki akwai jami’an lafiya biyu suka mutu a dalilin kamuwa da cutar korona a jihar.
Manasseh ya ce gwamnati ta yi wa mutum 34,472 gwajin cutar, mutum 2,034 suka kamu, sannan an sallami mutum 1,990 a jihar.
Bayan haka Manasseh ya ce jihar ta yi nasarar rage yawan mace-macen mutane daga cutar daga kashi 7% zuwa Kashi 2.1%.
Ya hori mutanen dake cewa babu cutar da su yarda da lallai fa akwai cutar kuma su kiyaye sharuddan kaucewa kamuwa da cutar.
Manasseh ya kuma yi kira ga mutane da su yi allurar rigakafin cutar korona cewa yin haka na samar wa mutum kariya daga kamuwa da cutar.
Zuwa yanzu jihar ta yi wa mutum 36,932 allurar rigakafin korona.
Manasseh ya ce gwamnati za ta maida hankali wajen horas da jami’an lafiya a jihar domin inganta kiwon lafiya a jihar.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 120 da suka kamu da cutar a Najeriya ranar Talata kuma babu wanda cutar ta kashe a wannan rana.
Yanzu mutum 164,423 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 154,406 sun warke, 2,061 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 7,956 ke dauke da cutar.