Daliban jami’ar jihar Kaduna sun bayyana cewa ba za su amince da karin kudin makaranta da gwamnatin jihar Kaduna ta yi a cikin wannan mako.
Gwamnatin Kaduna karkashin gwamna Nasir El-Rufai ta kara kudin makarantan dalibai a jami’ar ninkin ba ninkin.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta ruwaito cewa daliban sun yi dafifi a ofishin Darektan kula da al’amuran dalibai na jami’ar in da suka bayyana ra’ayoyin su da mika koken su ga mahukuntar Jami’ar.
Kamar yadda sabon tsarin ya ke, dalibai ‘yan asalin jihar dake biyan naira 24,000 zuwa 26,000, za su rika biyan naira 150,000 har zuwa naira 500,000 musamman ga masu karatun aikin likitanci kuma ba ‘yan jiha ba.
Wani dalibi dake karatu a fannin kimiyyar zamantakewa a jami’ar Abdulrazak Shuaibu, ya ce yana biyan kudin makaranta naira 24,000 amma yanzu kwatsam sai ya ji an yi kari zuwa naira 150,000, wai ma don yana dan asalin jihar Kaduna kenan.
Shiko Shuaibu cewa ya yi a baya ana biyan naira 24,000 ga dalibai da ke karatun koyon aikin likitanci, amma yanzu an kara zuwa naira 300,000 ga yan asalin jiha, wanda ko ba yan asalin jiha bane za su biya naira 500,000 ne.
” Tsakani da Allah yaya iyayen mu za su iya biyan wadannan kudade, bayan wasu ma an kore su daga aiki a jihar, sannan ga matsin da annobar korona ta jefa iyaye da dama. Wasu ma hatta abincin da za su ci yana gagaran su, yanzu kuma sai a bijiro da karin kudin makaranta da rana tsaka.
A karshe sbhugaban jami’ar farfesa Abdullahi Ashafa ya godewa daliban yadda suka bayyana korafin su cikin lumana ba tare da tashin hankali ba.
Ya ce gwamnati tayi haka domin ta iya samarwa dalibai ilimin da za su yi alfahari da. Ya ce za a ci gaba da duba korafin na su.
Daga baya, jami’in hulda da jama’a na jami’an, Nuhu Bargo a wata takarda da ak yada a shafukan yanar gizo, ya bayyana cewa ba a bayyana sabon farsashin kudin makarantan ba tukunna, saboda haka wanda dalibai ke fadi ba daga gwamnatin jihar ya fito ba.