Yadda mutuwar Idris Deby za ta iya shafar tsaron Najeriya – Gwamnatin Tarayya

0

Mutuwar Shugaban Chadi Idris Deby za ta iya dagula matsalar tsaro a kasashen da ke makwautaka da kasar, kamar Najeriya.

Gwamnatin Tarayya ce ta bayyana haka a ranar Alhamis, ta bakin Ministan Tsaron Najeriya Manjo Janar Mai Ritaya, Bashir Magashi.

Ministan Tsaro Bashir Magashi ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a Fadar Shugaban Kasa, a Abuja.

Idris Deby dai ya kasance abokin gambizar Najeriya wajen yaki da ta’addanci a tsawo shekaru goma da Boko Haram su ka shafe su na fitinar Najeriya da Nijar, Chadi da Kamaru.

KISAN IDRIS DEBY: Fargabar Kwararowar ’Yan Gudun Hijira Cikin Najeriya -Magashi

Magashi ya bayyana cewa Najeriya za ta gaggauta daukar matakin ganin cewa rikicin Chadi bai shafi Najeriya ba, ta hanyar kara girka dakarun sojoji a kan iyakokin ta, musamman ma kan iyakar kasar da Chadi.

“Idan aka ce babu tsaro kwata-kwata a Chadi, to sauran kasashen da ke makautaka da ita sun bani sun lalace. To godiyar mu ita ce mu na da yarjejeniyar sojojin hadin-guiwa ta MJTF, wadda mu ke sa ran za ta ci gaba da dorewa. Amma kuma duk da haka, mu na cikin damuwa da yin kaffa-kaffa dangane da kan iyakokin mu da kasar Chadi, biyo bayan halin da kasar ta tsinci kan ta.

“Yayin da mu ka samu labarin kisan da aka yi wa Shugaban Chadi, mun san cewa to fa ga wata sabuwar guguwar matsala can ta darkako kasashen da ke makwautaka da Chadi, musamman ma Najeriya ita ce rashin wannan shugaba a Chadi zai fi shafa.

“To amma mu na godiya ga Allah cewa mu na da yarjejeniyar sojojin hadin giwa ta MJTF tsakanin Najeriya, Chadi, Nijar da Kamaru. Kuma dukkan mu irin damuwa daya mu ke nunawa ta rashin Shugaba Idris Deby.”

“Za mu kara karfafa dakaru a kan iyakokin mu domin tabbatar da cewa masu gudun hijira daga Chadi ba su yi ambaliya cikin Najeriya ba. Kai hatta ‘yan Najeriya da ke cikin kasar Chadi, na tabbata za su so dawowa gida Najeriya.

“Kun ga kenan tashi tsaye mu yi kwakkwaran shiri ya same mu. Mu shirya domin dawowar ‘yan Najeriya da ke Chadi da kuma hana kwararowar ‘yan kasar Chadi cikin Najeriya.’’

KISAN IDRIS DEBY: Fargabar Fantsamar Muggan Makamai A Najeriya – Magashi

Mu na kuma cike da fargabar fantsamar muggan makamai cikin Najeriya. Kafin yanzu, dama Chadi ce ke hanawa da dakile shigo da muggan makamai cikin Najeriya.

“To yanzu kuma kuma kai-tsaye tun daga Libya har cikin Najeriya ana iya shigo da makamai, kamar yadda ake safarar dabino a saukake, saboda babu wani zare idanu da Chadin za ta yi a kan hanyar safarar makaman.

“Don haka tilas sai mun dauki matakan dakile wannan safara, Kuma mu na kan bakin kokarin yin haka din, mun ma kamo hanyar tabbatar da hakan. Mu na dai ta kara addu’a cewa kasashen Afrika za su samo lakanin hana matsalar kasar Chadi dagulewa, ta yadda za a samu kwakkwarar al’umma nagartacciya maicike da zaman lumana a Afrika.”

Share.

game da Author