Kungiyar kwadago NLC ta sanar da tafiya yajin aikin kwanaki biyar a dukkan ma’aikatun gwamnati da masu zaman kan su da ke jihar Kaduna, domin nuna rashin amincewar su da matakin korar dubban ma’aikatan jihar da gwamnati ta yi.
Da yake yi wa manema labarai karin bayani bayan kammala wani taro da kungiyar kungiyar tayi a Abuja ranar Alhamis, shugaban kungiyar kwadago Ayuba Wabba, ya ce bayan wanda za a yi na kwanaki biyar wanda za su tabbata komai ya tsaya cak a jihar Kaduna, idan gwamnati bata ce komai ba kuma za a shiga yajin aiki gadan gadan sai wada ta yiwu.
” Ba da dadewa ba an kori dubban ma’aikatan Kananan hukumomi ba tare da an bi ka’idar korar ma’aikatan ba. Sannan kuma gwamnatin jihar Karkashin gwamna Nasir El-Rufai sun sake bijiro da korar ma’aikata, wai babu kudin yin ayyuka.
” Mun sani cewa jihar Kaduna na daga cikin jihohin dake karbar kaso mai tsoka daga gwamnatin tarayya, yay a za a ce wai ba za a iya biyan ma’aikata ba sai an zaftare su tukunna.
” Duk wani magana na rashin kudi, zancen kanzon kurege ne kawai a jihar Kaduna. Nan ba da dadewa ba jihar ta fito tana kurin wai ta samu jibgin kudaden shiga da suka kai har naira biliyan 50 a shekara, kuma wai sai ace sai an zaftare ma’aikata ne za a iya biyan su albashi. Ba za mu yar da da haka ba.
Wabba ya ce wannan zanga-zanga da yajin aiki zai yi tsanani kuma ya kamata duka ‘yan Najeriya su mara wa baya domin illolin dake tattare da shi. Mun yi wa gwamnatin jihar wasika game da abinda ya taso amma ba ta ce komai ba.