Kotun Daukaka Kara a Gombe ta umarci a sake shari’ar tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha tare da wasu mutum hudu da ake zargin su da yi wa naira milyan 450 taron-dangin da su ka lamushe ta.
Hukumar EFCC dai ta zargi tsohon Minista Abdu Bulama da sauran wadanda ake zargib su hudub tare da shi cewa su karbi wani kaso daga cikin kudaden da Diezani Alison-Madueke ta raba domin a karkatar da zaben 2015 yadda zai yi wasu Diezani dadi.
Tun farko dai wani Mai Shari’a mai suna Isa Dashen da ke Babbar Kotun Tarayya a Damaturu ne ya kori karar tare da sallamar wadanda ake zargin.
Sai dai kuma wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na EFCC. Wilson Uwujeren ya fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa Kotun Daukaka Kara ta zartas da hukuci a ranar 3 Ga Maris cewa a sake shari’ar tun daga farko.
Kotunn Daukaka Kara ta ce a maida karar a hannun wani Alkalin Babbar Kotun Tarayya daban, ba a hannun Isa Dashen, wanda ya kori karar ba.
An dai gurfanar da tsohon minista Bulama da wasu mutum hudun da ake zargin su tare da yinn wuru-wurun naira miyan 450.
EFCC ce ta gurfanar da su a gaban Mai Shari’a Isa Dashen a ranar 18 Ga Mayu, 2018.
Sauran wadanda ake tuhumar su tare da Minista Bulama sun hada da Mohammed Kadai, Abba Gana Tata, Muhammad Mamu da kuma Hassan Ibn Jaks.
Kafin Mai Shari’a Dashen ya kori karar, sai da EFCC ta gabatar da shaidu shida tare da damka wa kotu takardun hujjar cewa wadanda ake zarfin sun karkatar da kudaden har naira milyan 450.
Duk wadannan tulin hujjoji sai Mai Shari’a Isa Dashen ya sallame shi, lamarin da bai yi wa EFCC dadi ba, har ta daukaka kar zuwa Kotun Daukaka Kara da ke Gombe, a cikin Maris 2021.
Mai Shari’a Tunde Awoteye na Kotun Daukaka Kara a Gombe ya umarci sake shari’ar tun daga farko, amma a dauke ta daga hanun Isa Dashen, a dasa ta hannun wani alkalin Kotun Tarayya na daban.