HARKALLAR NAIRA BILYAN 2: Dalilin da ya sa na janye daga kare Maina a kotu – Babban Lauya Sani Katu

0

Mashahurin Lauya a Najeriya Sani Katu, ya bayyana wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja cewa ya janye daga kare Abdulrasheed Maina, tsohon Shugaban Kwamitin Yi wa Fansho Garambawul.

Ya bayyana a cikin takardar da ya bayyana wa kotu cewa ya janye ne saboda fahimtar sa da ta Maina da kuma tunanin sa da na Main aba su zo daya ko daidai ba.

Katu ne lauya na uku da ya janye daga kare Maina a cikin watanni uku.

A ranar Laraba ce ya nemi kotu ta sahale masa janyewa daga kare Maina, amma sai Mai Shari’a Okon Abang, ya bayyana cewa ba zai iya janye a lokacin da ya sanar da kotu ba, tilas sai ya sanar kwanaki uku kafin ranar janyewar ta sa, domin ya bai wa kotu lokaci.

Abang ya ce haka doka ta shar’anta kan lauyan da ke kare wanda ake tuhuma da aikata laifi.

To daga nan kuma sai lauyan ya bi umarnin kotu, ya rubuta takardar neman janyewa daga ranar Laraba, ya ce ya daina kare Maina.

A cikin wata kwafen takardar da aka aika wa kotu, wadda PREMIUM TIMES ta ci karo da ita, an ambaci kalmar “cuta”, sai dai kuma ba a kara yin wani bayani daga nan ba.

“Wasu hujjoji sun nuna cewa da wanda ake karar da shi wanda ke kare shi din ba su yi amanna da juna a fahimtar iri daya kan lamarin ba.”

Katu ya kara da cewa ya janye don haka sai shi wanda ake kara ya kawo lauyan da ya ga dama kuma wanda ya fi kwanta masa a rai, domin ya ci gaba da kare shi.

Yayin da ba a san dalilin yanjewar ta sa ba, amma kuma PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa Babban Lauya Sani Katu bai ji dadi ba, kuma bai goyi bayan yadda wani a cikin lauyoyin Maina ya sa kotu ta tura sammaci ga Ministan Shari’a Malami, Magu, Emefile ba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin aika wa su Malami da wasu mutum takwas sammaci.

Rahoton ya ce Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta amincce da bukatar tsohon Shugaban Kwamitin Garambawul din Hukumar Fansho, Abdulrasheed Maina, wanda ya roki kotu ta kira Ministan Shari’a Abubakar Malami, Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, domin su amsa tambayoyin kotu.

Sauran wadanda aka gayyata din bayan rokon da Maina ya yi, sun hada da tsohon Shugaban Rikon EFCC, Irahim Magu da kuma Lauya Femi Falana.

Mai Shari’a Okon Abang ya aika wa kowanen su sammace daban-daban, inda a ciki ya umarci da su bayyana a ranakun 9, 10, 11 da kuma 12 Ga Maris, domin su bayar da shaida.

Abang ya aika masu da sammacen bayyana domin bada shaida, bayan da Maina, wanda ake tuhuma da salwantar naira bilyan biyu ya nemi kotun ta yi haka.

Ana tuhumar Maina da karkatar da naira bilayn biyu daga cikin kudin fanshon ma’aikata.

Akalla sammace biyar Mai Shari’a ya aika wa mutane daban-daban, akasarin su manyan jami’an gwamnati bayan da Maina ya bukataci kotun ta kira su, domin su gurfana su bayar da shaida.

Sauran wadanda aka aika wa sammacen sun hada da M. Mustapha da ke Zenith Bank, Abuja, Mohammed Wakili tsohon kwamishinan ’yan sanda da kuma Keneth Amabem.

Akwai Kennedy Uzoka, Shugaban Bankin UBA, sai Nneka Onyeali-Ikpe, da Shugaban Bankin Fedility, sai Ibrahim Kaigama na NIPPSS, Jos da kuma Daraktan tabbatar da Bin Ka’ida na Babban Bankin Najeriya, CBN.

“Ana umartar ku da ku bayyana a wannan kotu mai lamba 6, ranar 9, 10 da 11 karfe 9 na safe, a wannan ranakun har sai gunadar da wannan shari’a wadda shi wanda ake tuhuma ne ya nemi ku zo ku bayar da shaida.

“Ku sani ana gayyatar ku ne a bisa madadi da umarnin Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Najeriya.”

Allura Na Neman Tono Garma: Dalilin Makalo Malami, Magu, Falana da ICPC Cikin Harkallar Maina:

Mai bayar da shaida a bangaren wanda ake kara domin kare shi, Ngozika Ihuoma ne ya ambaci sunayen su daya bayan daya a kotu.

Misali: Ihuoma ya yi ikirarin cewa Maina ya hadu da Malami da Mashawarcin Shugaban Kasa a Harkokin Tsaro a Dubai cikin 2016.

Ya ce “Maina ya bai wa Malami da Hukumar NSA wani rahoto na sirri, wanda ya yi sanadiyyar bankadowa da kwato wasu naira tiriliyan 1.3.”

Ya kuma yi ikirari a kotun cewa Kwamitin Fansho na PRTT a karkashin Maina ya kwato naira bilyan 282, wadanda aka ajiye a CBN. Wannan shi ne dalilin gayyatar Emefiele na CBN.

Sannan kuma mai bayar da shaidar kariya cewa Maina bai ci kudi ba, ya ci gaba da cewa an yi amfani da kudaden da Kwamitin Maina ya tara, inda aka ciri naira bilyan 74, aka zuba cikin kasafin kudin 2012.

Sannan ya kara da cewa Maina ya bai wa Hukumar ICPC rahoton sirri dangane da yadda ake kokarin karkatar da wata naira bilyan 35 daga ofishin tsohuwar Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Winifred Oyo-Ita.

Share.

game da Author