Akalla mutum 937 ’yan bindiga su ka kashe a Jihar Kaduna cikin shekarar 2020.
Wani rahoto kan batun matsalar tsaro a jihar ne ya tabbatar da haka, kamar yadda Kwamishinan Harkokin Tsaro Samuel Aruwan ya tabbatar.
Aruwan ya kara da cewa kuma bayanan da gwamnatin jihar ta tattara, sun tabbatar da cewa an yi garkuwa da mutum 1,972 a cikin 2020 din.
Rahoton wanda aka fitar a ranar Laraba, ya dora laifin kisan kan masu garkuwa da ’yan bindiga da kuma sauran masu aikata sauran muggan laifuka daban-daban a Jihar Kaduna.
“Bangarorin addinai da kabilu daban-daban duk sun dandana ukubar wannan kashe-kashe da garkuwa a Kaduna. Sannan kuma babu wata jam’iyyar siyasar da za ta ce ana ware wasu a kyale wasu. Kowa wannan matsala ta shafe shi.”
Aruwan ya kara da cewa, daga cikin mutum 937 da ’yan bindiga su ka kashe a Kaduna, an fi kashe mutane da yawa har 152 a Karamar Hukumar Igabi. Sai kuma Karamar Hukumar Kajuru da aka kashe mutane 144.
An kashe mutane 468 a Kananan Hukumomin Birnin Gwari, Igabi, Giwa da Chikun, wadanda kusan sun doshi kashi 50 bisa 100 na mutanen da aka kashe.
A Kudancin Kaduna an kashe mutum 286 sanadiyyar hare-haren ’yan bindiga da fadace-fadacen ramuwar-gayyar barnar da aka yi wa wani bangare a baya, musamman tsakanin watan Yuni zuwa Nuwamba, 2020.
Yayin da Gwamna Nasir El-Rufai ke karbar rahoton, ya babbaya cewa Gwamnatin Jihar Kaduna nab akin kokarin ta wajen yin amfani da dan kudaden shigar da ta ke samu ta na kokarin shawo kan matsalar tsaro a fadin jihar.
Sannan kuma ya ce Kaduna na aiki kafada-da-kafada da sauran jhohinn da ke makautaka da ita, domin ganin an dakile matsalar tsaro baki daya.
Sai dai kuma ya nuna takaicinnyadda korkarin haka kai tsakanin juna da jihohin su ka yi a cikin 2015 bai yi nasara ba.