Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko NPHCDA Faisal Shu’aib ya bayyana cewa zuwa yanzu an yi wa mutum 215,277 allurar rigakafin AstraZeneca a Najeriya.
Shu’aib ya fadi haka ne a shafin da na tiwita dake yanar gizo ranar Talata.
Ya ce jihar Legas ce ta fi yawan mutanen da aka yi wa rigakafin da mutum 58,461. Daga nan sai jihohin Bauchi- 23,827, Jigawa -20,800, Ogun – 19,257 da Kaduna -14,527.
Saura kuwa sun hada da Jihohin Ebonyi – 77, Sokoto – 98 da Akwa Ibom – 127.
Shu’aib ya ce har yanzu babu wani rahoton samun matsala ko da daya ne a kasar nan da aka fara yi wa mutane rigakafin korona.
Shu’aib ya yi kira ga yan Najeriya musamman masu fama da wasu cututtuka banda Korona da su garzayo wuraren da ake yin rigakafin Korona ayi musu.
Har yanzu ana ci gaba da wayar wa mutane kai game da ingancin wannan rigakafi.
Najeriya ta karbi akalla kwalaben ruwan maganin Korona din milliyan hudu, kamfanin sadarwa ta MTN ta tallafa wa Najeriya da kwalaben ruwan rigakafin 300,000.
A hankali dai rigakafin na ci gaba da samun karbuwa wajen yan Najeriya.