An haramta wa sojojin Najeriya watsa hotuna da bidiyo a soshiyal midiya ba da izni ba

0

Hukumar Sojojin Najeriya ta haramta wa sojojin kasar nan shiga soshiyal midiya su na watsa hotuna da bidiyo barkatai ba tare da izni ba.

“Duk wanda aka kama ya na tura hotuna a soshiyal midiya ko tura wasu bayanai to za a damke shi, a bincike shi kuma a hukunta shi.”

Babban Kwamandan Bataliya ta 81 Lawrence Fejokwu ne ya yi wannan gargadin a wurin taron sanin makamar aiki kan Dokokin ’Yancin Dan Adam a ranar Talata.

Manjo Janar Fejokwu ya kara da cewa ana samun yawaitar hotunan sojoji barkatar a soshiyal midiya wadanda yawancin su kuma sojojin ne da kan su ke watsa su.

Fejokwu, wanda ya yi magana ta yawun Shugaban Ma’aikatan sa, Burgediya Janar Nsikak Edit, ya bada misalin abin da ya faru lokacin hargitsin #EndSARS, wanda ya ce dole a saisaita sojojin bisa hanyar da ta kamata su rika mu’amala a soshiyal midiya.

“Haka kawai sai ka ga mutane su na tsaye su na daukar hotuna da bidiyon da za su iya amfani da su su na bayyana sojojin Najeriya a hanyar da ba ta dace ba, tare da bata masu suna.” Inji shi.

GOC din ya kara da cewa a wannan taron sanin makamar aikin, wajibi ne a koya wa sojoji yadda za su tabbar da cewa ba su rika rika daukar hoto ko bidiyo su na tura wa mutanen da ba su dace ba.

“Hotunan da ba su kamata a ce sun shiga soshiyal midiya ba, amma ga su can birjik duk an watsa. Kuma wasu da yawa sojojin mu ne su ka dauki hotunan, su ka watsa.”

Daratan Horaswa Nuhu Shuaibu ya kara da cewa za a kara horas da su yadda za su tabbatar su na gudanar da aikin su bisa ka’ida da kwarewa ba tare da daukar doka a hannu ba.

Share.

game da Author