Kwana daya bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi tsohon Gwamna Gbenga Daniel da tsohon Kakakin Majalisar Tarayya wadanda su ka sauya sheka zuwa APC, shi kuma tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose, ya yi wa shugaban wankin babban bargo.
Fayose ya zargi Buhari da yin watsi da matsalar tsaro, ya buge ya na taro da mutanen da ya kira ’yan yawon gantali.
Tsohon Gwamna Fayose ya shawarci Buhari ya mike tsaye kyam ya fuskanci gagarimar matsalar tsaron da ta dabaibaye kasar nan baki daya, ya rabu da taron ganawa da ’yan adawar da ke sauya sheka su na komawa APC.
Premium Times ta buga labarin sauya shekar da Bankole da Gbenga su ka yi zuwa APC, kuma ta buga labarin ziyarar da su ka kai wa Shugaba Buhari a Fadar Shugaban Kasa.
Sai dai kuma a raddin da Fayose ya ragargaje su, ya bayyana cewa tuni ’yan Najeriya sun gaji da irin su Gbenga Daniel a siyasa, domin sun zama “kayan rafter bola wadanda ake markada su a yi duk abin da ake son yi da su bayan sun rube.”
“Mutanen Najeriya ba su damu da kiran da Shugaban Kasa ke wa ’yan yawon gantalin siyasa ya na ganawa da su a fadar sa ba. Sun fi damuwa da gagarimar matsalar tsaron da ta addabe su kawai.”
“Ina ruwan mutanen Najeriya da son ganin wasu masu yawon gallafiri na shiga APC, matacciyar jam’iyya.”
“Zan so a ce Shugaba Buhari ya san yadda ’yan Najeriya su ka tsane shi a yanzu, saboda ya kai su ya baro. Ya shirga masu tulin alkawurran da bai ma kamo hanyar cikawa ba.”