Wata mace mai suna Eheduru-Onyejekwe da ke da gonar Mozani farms, ta bayyana yadda ta ke gudanar da harkokin noma da su ka hada da noma amfanin gona, kiwo da kuma harkokin hada-hadar kayan noma na zamani da kayan abinci.
Sannan kuma ta bayyana irin kalubalen da ke gaban su dangane da matsalar makiyaya.
Tashin farko dai ni na yi digiri na farko a fannin kidddigar kudade. Amma kuma tun daga 2011 na shiga harkokin noma gadan-gadan, har yanzu ina cikin tsamo-tsamo. Ina da maka-makan gonaki da kuma harkokin hada-hadar kayan noma na zamani.
“Sannan kuma ina kan aikin kaddamar da wata gona katafariya a jihar Oyo, mai fadin akalla eka 300 zuwa 400.
“Ina jan hankalin jama’a da dama cewa su tsunduma harkokin noma kawai, saboda al’ummar Najeriya sai kara yawa su ke yi. Sannan tashe-tashen hankula sai karuwa su ke yi, jama’a na ta guduwa cikin birni.
“To akwai alamomin za a yi yunwa saboda mahara da ‘yan bindiga don haka abinci zai yi karanci. Idan kuma ya samu, to tsada zain yi matuka sosai. Wannan fa idan aka yi la’akari da munin rashin tsaro a Arewa da kuma yadda matsalar ta ki ci ta kncinyewa.
“Saboda haka a tashi tsaye wajen harkokin noma, dama kuma noma a al’adar mu ce. Ba noman ne al’ada ba.
“Bari ku ji yadda na fara shiga harkokin noma. Lokacin ina jami’a, sai na je gonar baban wata kawa ta a Benin, inda ya ke yin man ja. A inda na ke tsaye a gonar, sai na fahimci akwai hanyoyin da za su iya inganta harkar ta su, tun daga kara yawan wanda su ke yi zuwa wurin adanawa da harkar sayarwa.
“Ina komawa gida sai na fara ni ma daga cikin gida na. na rika dasa bishiyar kwakwar man ja, amma sai su ki yi. Har guda 200 na dasa, amma sai beraye da zomaye su cinye.
“Na koma ina kiwon kaji, shi ma da farko na sha wahala, saboda bai karbe ni ba daga baya.
“Lokacin da na fara kiwon kaji, na fara da kaji 50 ina kiwon tare da mama ta. A karshe babu kajin, sai kudin 10 kadai ta ba ni. Na ce ina sauran? Aka ce min ai mahaifin ki ya cinye guda 10, uku sun mutu. Haka dai ta yi min lissafin yadda aka bai wa wani da yadda aka bai wa wata.
“Da na ga kiwon kaji a lokacin bai karbe ni ba, sai na saki na kama noman gurji, wato cucumber kenan, inda na shuka 500 tashin farko.
“To da kakar gurjin nan ta zo fa, ni na dauki buhu 40 na kai kasuwa na rika sayarwa da kai na. Daga nan kuma nasibin kasuwa ya bude mani.
“CIKIN 2017/2018 na fara harkar sana’ar noma gadan-gadan, har na je na yi diflomar watanni shida kan sanin makamar irin shuka, maganin kashe kwari da kuma cututtukan dabbobi.
“Bayan na gama sai na koma kiwon kaji, inda tashin farko na yi kiwon guda 10,0000.
“Cikin 2018 na yi wani kwas kuma na kama noma, inda na samu eka 300 na shuka gyada, masara, tumatir, barkono da sauran su.”
Ta bayyana cewa da haka ta fara har abu ya kankama sosai ta zama kasaitacciya.
A wannan tataunawa ta shaida wa wakilin mu cewa ba ta wata kungiyar mata manoma, kuma wani tallafi ko ramce bai taba shigowa a hanun ta ba.
Sannan ta ce akwai ma’aikata kamar 17 da ke aiki a gonakin ta ta na biyan su. Amma kuma a cikin su babu mace ko daya, saboda a cewar ta, mata ba su cika son aikin noma ba.
Ta na da gonaki a jihohin Oyo, Imo, Ribas da Jihar Nasarawa inda ta ke harkokin noma. Duk da dai wasu gonakin ba ita kadai ke da su ba, na hadin guiwa ne.
Yayin da wasu gonakin na su ne, ta bayyana cewa wasu gonakin kuma aro su ka biya su ka karba, abin da hausawa ke kira noma-tashi.