Yadda Minista Malami ya ki jin gargadin zargin harkalla ya rika kokarin a biya bashin naira biliyan 159

0

An shafe shekaru ba day aba, ba biyu ba, Ministan Shari’a Abubakar Malami na bijire wa gargadin da ake yi masa cewa wasu kudade da ya ke ta kokarin ganin an biya daga cikin kason kudaden Jihohi da Kananan Muhumomi har dala milyan 418 (naira biliyan 159), akwai gidoga a cikin lamarin.

Kudaden dai an ce wai bashi ne wasu ‘yan kwangila da jami’an tuntuba ke bin jihohi da kananan hukumomi.

Amma duk da gargadin da aka rika yi wa Malami, ciki kuwa har da rahoton da EFCC ta damka masa, wanda ta nuna cewa bashin haramtacce ne, ba gaskiya ba ne, shi kuma Minista Malami ya rufe ido sai matsa lamba ya ke yi domin ganin an biya wadanda aka ce wai su na bin bashin, ta hanyar rika cirar kudade ana biyan bashin daga kudaden da Gwmnatin Tarayya ke bai wa Johohi da Kananan Hukumomi a duk karshen wata.

Wannan jarida ta mallaki kwafe-kwafe na takardun da su ka rika karakaina da ke nuna yadda Malami ya rufe ido ya ke ta sharce gumin ganin lallai a biya kudaden, duk kuwa da cewa hatta Kungiyar Gwamnoni ta Najeriya, NGF ta bayyana masa cewa binciken kwakwaf ne kadai zai iya tabbatar da sahihancin bashin ko bogi da gidoganci ne kawai.

‘Yan Kakuduba Uku:

Sauran mutan biyun da su ka hada kai da Minista Malami domin ganin an biya kudaden ido-rufe, sun hada da Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari da kuma Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed.

Gungun Wasu ’Yan Gidoga:

Wato akwai wasu ’yan dillancin gidoga da ke ikirarin su ne wakilan masu bin bashin, wadanda wakilan mu su ka ji cewa sun yi kokarin su bai wa Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi toshiyar bakin dala milyan 40, domin ya hakura, ya daina tirjiya, ya amince a biya bashin kawai.

Amma Gwamna Fayemi din na Jihar Ekiti bai amince ba, ya ki karbar tayin da su ka yi masa, inda ya tsaya kai da fata cewa lallai sai dai a yi kwakkwaran binciken kwakwaf domin a gano gaskyar lamarin.

Sai dai kuma bayan da PREMIUM TIMES ta fallasa wannan kakuduba cikin makon da ya gabata, an rika daukar nauyin buga wasu bayanan bata suna ga Gwamna Fayemi a cikin kafafen yada labarai.

Cewa aka rika yi wai Fayemi an ki amincewa da rokon da ya yi na a datse kashi 10 cikin 100 na bashin.

Salsalar Wannan Hukuncin Biyan Bashi:

Batun wannan bashi da ake tankiya da tababar sa, ya samo asali ne daga wani hukuncin da kotu ta yanke cewa wasu ’yan kwangila da jami’an tuntuba na bin jihohi da kananan hukumomi 774 na kasar nanbasussuka.

Wasu ’yan gidoga su ka yi ikirarin cewa su jami’an tuntuba ne su ka ce sun taimaka wa kananan hukumoni da jihohi sun domin su karbo kudaden su da aka cira fiye da kima tsakanin 1995 da 2002 domin biyan bashin Paris Club.

Wasu ‘yan kwangila kuma daga cikin su wai sun yi wa kananan hukumomi 774 ayyuka bashi, saboda zaman jiran tsammanin za a biya kudaden Paris Club a biya su daga ciki.

A baya PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Shugaban Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomin Najeriya, ALGON ya nuna goyon bayan a biya kudaden.

Buhari Ya Sani Ya Yi Shiru:

PREMMIUM TIMES ta buga labari a cikin Janairu, yadda Kungiyar Gwamnaonin Najeriya ta kai wa Shugaba Muhammadu Buhari cewa kada ya bari a biya kudaden, domin babu wata kwakwarar hujjar an yi ayyukan bashin.

Sai dai kuma duk da wannan gargadin Buhari bai taka wa su Malami burki ba

Sai ma da ta kai ga Malami ya samu sakonnin gargadi daga wurare uku, ciki har da EFCC su na shaida masa cewa kada ya shiga gaba a biya bashin, domin akwai gidoga a ikin lamarin.

Cikin wadanda su ka gargadi Minista Malami har da Shugaban ALGON na baya-baya, wanda shi ma ya nuna cewa kamfanonin tuntuba masu cewa su ne dillalan wadanda ke bi bashi, ba su san da zaman su ba.

Yayin da su Malami su ka matsa lamba har Buhari ya sa hannu kan cakin kudin alkawarin biya (promisory note), a ranar 4 Ga Disamba, 2020, su ma Gwamnomin daga baya cikin Janairu sun samo wani sabon umarni daga Buhari cewa kada a bia kudaden, har sai an yi kwakkwaran bincike.

Har zuwa yanzu dai gwamnonin Najeriya ba su samu tabbataci daga bangaren su Gambari da Malami ba cewa shin za su bi umarnin da Buhari ya bayar, ko kuwa ba za su bi ba?

Share.

game da Author