Tantance korafin Sanata Dino game maganin rigakafin Korona na Astrazeneca – Binciken DUBAWA

0

Wani tsohon dan majalisa a Najeriya ya yi korafin rashin ingancin maganin rigakafin Korona na kamfanin AstraZeneca.

Zargi: A wani bidiyon da ya wallafa a shafukansa na Instagram da Twitter, tsohon dan majalisa sanata Dino Melaye ya ce Najeriya ba ta yi zabi mai kyau ba da ta zabi allurar rigakafin COVID-19 daga kamfanin magunguna na AstraZeneca.

Yayin da ake hankoron ganin an samar da allurar rigafin COVID-19, Najeriya ta karbi ruwan maganin miliyan 3.94 na AstraZeneca/Oxford. Ranar biyu ga watan Maris 2021 allurar ta iso daga COVAX, wanda gamayyar hadin guiwa ce tsakanin CEPI Gavi, UNICEF da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

Cibiyar magunguna ta Serum (SII) da ke Indiya ce ta sarrafa allurar AstraZeneca/Oxford wa COVAX. COVAX shi ne ginshikin samar da allurar rigafin na COVID-19 domin aikin shi she ne ya kula da sarrafawa da samar da allurar rigakafin, ya kuma tabbatar cewa kowa ya sami damar yin gwajin ko yana/tana dauke da COVID-19. Idan kuma an yi gwajin an sami mutun da cutar, COVAX zai tabbatar an samar da magani ba tare da nuna wariya ko banbanci ba.

Dan haka ne COVAX ya kaddamar da wata hanyar samar da kudi da ake kira Advanced Market Commitment (AMC). Wannan yarjejeniya ce da aka yi a hukumance dan rage farashin allurar rigakafin wa kasashe marasa karfi da masu matsakaicin karfi musamman dan cutar na da saurin hallaka mutane. Wannan mataki da aka dauka zai tallafawa kasashe 92, marasa karfi da masu matsakaicin karfi a Afirka.

Najeriya ta kasance daga cikin wadannan kasashe, kuma ana sa ran samar da kason farko na magungunan su kai ga wadannan kasashen baki daya cikin watanni hudu na farkon wannan shekara ta 2021.

Ghana ce ta fara samun magungunan, inda ta sami guda 600,000 sai Ivory Coast na biye da ita da guda 500,000. Najeriya ce ta sami mafi yawa daga cikin kason farkon, kuma ta na sa ran samun milliyan 16 baki daya, daga cikin adadin da za’a rabawa kasashen 92, sau hudu.

Allurara AstraZeneca na da mahimmanci sosai. Na farko dai ba ta da tsada. Ana saida ta a kan pound 2.50 kowace kwalba. Dan haka za ta fi saukin sha’ani musamman saboda adadin kasashen da ake so a baiwa kyauta na da yawa. Bacin fargabar da Afirka ta Kudu ta nuna bayan da ta ki amincewa da allurar, ana ganin AstraZenecan za ta fi dacewa da kasashe masu tasowa kamar Najeriya tunda akwai arha, kuma ana iya ajiye ta a kowani irin Firji ba kamar Pfizer da Moderna ba wadanda ke bukatar sanyi sosai daga -20 zuwa -70 bisa ma’aunin Celsius.

Ranar talata wani mai amfani da shafin Instagram mai suna Tunde Ednut @kingtundeednut ya wallafa bidiyo mai tsawon miniti biyar da sakan shidda, na sanata Dino Melaye ya na sukar gwamnati a kan allurar ta AstraZeneca.

A cewar sanatan, Najeriya ta yi zaben tumun dare da ta zabi AstraZeneca domin a duk cikin allurai hudun da WHO ta amince a yi amfani da su a duniya, ita ce ba ta karfi kuma ta fi kowane hadarin janyo illoli. Sanatan ya ce bayan mutun ya karbi allurar zai iya samun zafin jiki, ciwon kai, gajiya, ciwo a naman fata, zazzabi, sanyi, da zafin kashi musamman a mahada sannan da amai.

Melaye ya kuma yi zargin cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya ware nera biliyan 300 dan wannan allurar rigakafin.

“Gwamnatin Najeriya ba ta yi wa Najeriya zaben kirki ba. Akwai allurai hudu. Wanda ya fi rashin karfi cikinsu gwamnatin ta zaba. Wannan ne kuma ya fi yi ma mutane illa. Idan muka duba sakamakon gwajin kaifin alluran hudu da aka yi, za mu ga cewa kaifin AstraZeneca wajen inganta garkuwar jikin mutun ya tsaya ne a kasha 62 cikin 100 bayan kwanki 14 da yin allurar. A yayin da Pfizer yake kashi 95 cikin 100 bayan kwanaki 28 bayan an yi allurar kasha na biyu. Moderna na kashi 94 cikin 100 a yayinda Johnson and Johnson ke kashi 74 cikin 100. CBN ta ware nera dubu billiyan 300 dan wadannan allurai, wannan babban kuskure ne kuma bai kamata ba. Ba su kyauta ba da suka zabi wannan allurar.”

Tantancewa:

Binciken ya kai ta shafin Twitter na sanata Dino Melaye, inda shi kansa ya wallafa labarin hade da wani jadawali. A cewar Dino “allurar rigakafin Indiyar da gwamnatin tarayya ta kawo kasar nan ce mara karfi a cikin duka alluran da aka yi.”

A bidiyon da Tunde Ednut ya wallafa a Instagram, akwai tambarin tashar talbijin din Roots, dan haka Dubawa ta sake wani binciken a shafin YouTube inda ta ga bidiyon a shafin Roots.

Zargi na 1: Allurar rigakafin daga Indiya ne

Wani kamfanin magungunan Birtaniya ne ya kirkiro allurar rigakafin AstraZeneca tare da hadin gwiwar jami’ar Oxford, sannan cibiyar magunguna ta Serum da ke indiya ce ta sarrafa shi a karkashin lasisin da aka yi wa allurar.

Allurar ta kunshi wani nau’i ne na kwayar cutar da kan bulla a biri, sai dai an alkinta shi da wani bangare na kwayar cutar COVID-19 domin ya bunkasa garkuwar jikin mutun. Da zarar ta shiga kwayoyin jikin mutun, allurar za ta fara samar da wasu kwayoyi masu kare garkuwar jiki daga COVID-19

Ranar 15 ga watan Fabrairu, WHO ta sanar da allurar rigakafin AstraZeneca/Oxford iri biyu wadanda za a iya amfani da su cikin gaggawa. Matakin da ya baiwa COVAX damar fara raba allurar rigakafin.

Zargi na 2: Allurar rigakafin na tattare da illoli kuma ita ce mai mafi karancin karfi wajen kare garkuwar jikin mutun.

Zargin cewa AstraZeneca ita ce mai mafi karancin karfi idan aka gwada ta da Pfizer da Morderna da Johnson and Johnson gaskiya ne, to amma wannan baya nufin cewa allurara bata aiki gaba daya. Duk da cewa alkaluma sun nuna karfin maganin a kan kashi 62.1 cikin 100, wannan adadi a tsakanin mutanen da suka karbi allurai biyu na maganin mai matsakaicin karfi ne. A wadanda suka fara da mai karamin karfi sannan aka basu mai matsakaicin karfi, alkaluman sun nuna cewa karfin maganin ya kai kasha 90 cikin 100.

Zargin cewa maganin na tattare da illoli karya ne domin WHO ba za ta ce a yi amfani da allurar da ke da illa ba tare da ta tantance karfin shi ba. Daya daga cikin takardun WHO na nuna cewa allurar na da karfin kashi 63 cikin 100.

Haka nan kuma a cewar wata kasidar likitoci mai suna Lancet Medical Journal, wanda ta wallafa ranar 8 ga watan Disemba 2020 allurar na aiki. Alkaluman da ta yi amfani da su sun nuna cewa tsakanin 23 ga watan Afrilu zuwa 4 ga watan Nuwamba 2020, mutane 23,848 suka gwada allurar rigakafin sannan wasu 11,636 sun kasance a gwajin da aka yi na tantance karfin aikin allurar rigakafin.

Wannan na nuna cewa allurar rigakafin AstraZeneca yana iya rage yaduwar cutar sosai ta rage kaifin ciwon a jikin mutanen da suka kamu da cutar sosai.

Bayan haka, ministan lafiyar Najeriya Osagie Ehanire ya ce WHO ta amince a yi amfani da allurar rigakafin idan har ba nau’in Afirka ta Kudu ne mai dauke da cutar ke da shi ba.

“Mun tambaye WHO, “Me za mu yi yanzu?” suka ce “dan har ba ku da nau’in Afira ta Kudu kuna iya amfani da shi”, wani jami’I ya bayyana mana. “Bamu da nau’in ke nan muna iya amfani da she.”

Duk da cewa allurar ba ta aiki a kan nau’in na Afirka ta Kudu, tana aiki sosai a mutanen da ke da cutar kadan zuwa matsakaici a Birtaniya, wanda kuma ake gani a Najeriya.

An riga an raba allurar a kashen Afirka guda 12 saboda haka ba yadda za’a yi.

Zargi 3: CBN ta ware nera Biliyan 300 wa allurar rigakafin

Sanatan ya ce duk da nera biliyan 300 da aka ware an je an dauki allurar rigakafi mara karko. Wannan karya ne domin duk yunkurin da CBN ya yi wajen dakile COVID-19 da ma allurar rigafin bai kai nera billiyan 300 ba. Da farko CBN ta bayar da nera billiyan 10 dan kirkiro allurar rigakafi a Najeriya sai kuma wani nera milliyan 253.4a karkashin shirin bankin na tallafawa sashin lafiya wajen bincike dan shawo kan annobar ta coronavirus.

Zargi 4: AstraZeneca ya fi sauran alluran illoli

Wannan zargin ba gaskiya ba ne. Lokacin da aka gwada AstraZeneca, illoli kalilan ne aka danganta da shi kuma duk sun waste bayan kwanaki kadan.

Haka kuma illolin da aka fi samu bayan allurar sun hada da ciwon kai, gajiya, sanyi, zazzabi, da amai. Wadannan illoli iri daya ne da na Pfizer, Moderna da Johnson and Johnson. Mutun daya ne daga cikin mutane 23,754 din da suka gwada maganin mutun daya ne ya sami matsaloli masu kaifin gaske.

A Karshe

Zargin da sanatan ya yi, ya kunshi gaskiya da karya. Duk da cewa da gaske ne a Indiya aka sarrafa allurar rigakafin kuma ba kai karfin sauran alluran ba, allauran rigakafin yana aiki kuma illolin ba su ne mafi muni ba. Haka nan kuma babban bankin Najeriya bai ware nera biliyan 300 dan alluranba, wadanda aka samu yanzu kyauta aka karba daga COVAX. Cibiyar hadakar hukumomi da kasashen da ke raba allurar rigakafin ga kasashe marasa karfi.

Yayinda ake cigaba da raba allurar rigakafin, za’a rika samun bayanai na karya da kuma masu karo da juna amma za mu cigaba da gudanar da bincike dan mu tabbatar kun sami gaskiya.

Share.

game da Author