Za a gina karamar tashar wutar lantarki domin wasu masana’antun Kano

0

Gwamnatin Tarayya ta sanar a ranar Juma’a cewa ta sa hannun kulla yarjejeniyar gina karamar tashar wutar lantarki mai zaman kan ta, mai karfin migawat 25 a Kano.

Sai dai kuma karamar tashar za a gina ta ne domin amfanin masana’antun da ke bangaren Kasuwancin da babu Talala da Haraji wato ‘Kano Free Trade Zone (KFTZ).

Wutar wadda wani kamfani mai zaman kan sa ce zai gina tashar ta, ana sa ranar daga zanar da za a fara ginin, za a dauki watanni 11 kacal a kammala aikin baki daya.

Ministan Cinikayya da Masana’antu Richard Adeniyi-Adebayo ne ya bayyana haka a Kano, lokacin da ya kai ziyara a rukunin KFTZ.

Ya kuma kara da cewa Gwamnatin Tarayya ta fito da wasu tsare-tsare masu fa’ida sosai, wadanda za su samar da yanayi na samun masu zuba jari sosai a KFTZ.

“Mu na zuba makudan kudade wajen samar da kayayyakin inganata rayuwa, amma babbar matsalar da duk wani mai zuba jari ko sha’awar zuba jari, ita ce matsalar wutar lantarki. Jama’a su na bukatar wutar lantarki a bangarorin da za su zuba jari. Don haka idan aka samu wutar lantarki, to wannan bangare zai bunkasa.

“Tuni mu ka samu kamfanoni da dama wadanda su ka nuna aniyar su ta zuba jari a nan. Mu na ma kokarin kara fadada filayen da za a gina masana’antu dama dama.’’

Ya ce ma’aikatar sa na tattaunawa da Hukumar Sayar da Kadarorin Gwamnati (BPE), amma dai har yanzu ba cimma matsaya a kan sayar da FTZ na Kano da Calabar ba.

Share.

game da Author