A yi kaffa-kaffa da wasu ’yan yunwa da marasa mutunci masu tururuwa cikin APC -Aregbesola

0

Tsohon Gwamnan Jihar Osun, kuma Ministan Harkokin Cikin Gida a yanzu, Rauf Aregbesola, ya nuna damuwa dangane da yadda wasu masu tururuwa su na shiga jam’iyyar APC a yanzu, saboda yunwa ta rarake masu ciki a siyasance.

Aregbesola ya yi wannan gargadi ne daidai lokacin da wasu shugabannin jam’iyyar APC su ka nuna damuwar su dangane da ficewar da ya yi daga SDP ya koma APC.

A ranar Litinin ce PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Omisore ya yi rajisrar jam’iyyar APC mazabar Moore, Ile-Ife, tare da dimbin magoya bayan sa su na kambama gwamnan da ke kai, tare da cewa, “Oyetola sai ka yi zango na biyu.”

Omisore dai ya yi takarar gwamna a karkashin SDP a zaben 2018, inda ya zo na uku.

Sai dai kuma ya goya wa Gboyega Oyetola na APC wanda ya yi nasara kan Ademola Adeleke na biyu na jam’iyyar PDP, wanda ke gaba da kuri’u 353 kafin a a yi zaben da bai kammalu ba a wasu mazabun da aka kayar da PDP din.

Sai dai kuma duk da mutuncin siyasar da Omisore ya yi wa APC, inda a zaben da bai kammalu ba ya goya baya APC ta kayar da PDP da kuri’u 462, wasu jiga-jigan APC ba su nuna goyon bayan komawar Omisore APC ba.

Yayin da ya ke maida martani kan yadda wasu ke komawa APC, tsohon gwamnan Osun ya ce kwansitushin ta Najeriya ta bai wa kowane tantirin da ake zargi da kuma masu kashe mutane ’yancin su shiga duk jam’iyyar da su ke so.

Ya yi wannan bayani a lokacin da ya je sabunta ta sa ku rajistar APC a maaba ta 8, a Ifofin, Karamar Hukumar Ilesa ta Gabas, jihar Osun.

“To amma zai fi kyau jam’iyya ta kasance wadanda ke mafiya rinjaye a cikin ta, mutane ne masu mutunci kuma nagari masu nagarta, kamar yadda jam’iyyar APC jam’iyya ce ta mutane nagari.”

“Tilas ya kasance akwai bambanci tsakanin masu kishin jam’iyya komai ruwa komai iska su kasance ba daidai su ke da ‘yan miya-ta-yi-zakin ba.” inji Aregbesola.

Duk da Aregbesola bai fadi sunan ko mutum daya ba, to amma dai tsohon sanata Omisore ana zargin sa da hannu a kisan Tsohon Ministan Shari’a, Bola Ige. Amma dai ya karya zargin.

Omisore ya yi mataimakin gwamna ga Gwamna Bisi Akande tsakanin 1999 zuwa 2003. Kuma ya yi Sanata tsakanin 2003 zuwa 2011.

Omisore ya sha kaye ga zaben gwamna a 2014 ga Aregbesola, kuma ya kara shan kaye a zaben 2018 ga Oyetola.

Share.

game da Author