Boko Haram sun arce da wasu jami’an kwastan har su uku a garin Geidam a wani hari da suka kai ranar Talata.
Maharan sun afka garin Geidam da yammacin Talata ne.
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa Boko Haram sun sammaci jami’an ne basu san zasu afka musu a inda suka ba.
Jami’an na aikin a shigen binciken motoci dake shiga gari ne maharan suka afka musu, in ji wani jami’i.
” Jami’an mu sun samu labarin zuwan Boko Haram kuma dukkan su sun kauce kafin su iso. Wadannan ukun basu samu wannan labari ba sai da suka iso gabdagab da Boko Haram kafin su ankare Boko Haram sun rufa da su.