Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa yawan masu zabe a Najeriya bai fi kashi 30 zuwa 35 cikin dari na wadanda su ka yi rajista a zagaye biyu na zabubbukan da aka yi na baya-bayan nan ba.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen taron tuntuba na farko da hukumar ta shirya tare da kungiyoyi masu zaman kan su (CSOs) na shekarar 2021 wanda aka yi a ranar Talata, a Abuja.
Yakubu ya ce a yayin da wasu zabubbukan sun fi samu yawan fitowar masu zabe, a wasu kuma ba a samu fitowar mutane sosai ba.
Ya ce, “A lokutan zagaye biyu na zabe da aka yi na baya-bayan nan, ciki har da zabubbukan da aka yi ba a lokutan da aka saba yin zabe ba, fitowar masu zabe don kada kuri’un su a sassan kasar nan ya tsaya ne tsakanin kashi 30 zuwa 35 cikin dari.
“A yayin da a wasu zabubbukan an fi samun fitowar masu zabe fiye da wasu, wasu zabubbukan cike gurbi da aka yi a watannin baya sun samu karancin masu fitowa don su kada ƙuri’un su da wajen kashi 8.3 cikin dari a mazabun da ke cikin birane wadanda ke da masu zabe da su ka yi rajista da su ka kai sama da miliyan 1.2 a birnin da ya fi kowanne cinkoson yawan jama’a.
“Wannan ba abin dadi ba ne idan an kwatanta shi da yadda masu zabe kan fito akalla kashi 65-70 cikin dari a wasu kasashen, har ma a yankin Afrika ta Yamma.”
Shugaban na INEC ya ce gaskiya ne kungiyoyi masu zaman kan su sun sha yin kira ga hukumar da ta nemo hanyoyin magance matsalar.
Yakubu ya ce a matsayin su na masu sa ido kan harkokin zabe da aka amince da su, wasu daga cikin kungiyoyin sun mika wa hukumar rahotanni, ya na mai karawa da cewa bayan hukumar ta yi wa rahotannin kyakkyawan nazari, sai ta fahimta sosai cewa sun damu ne da yadda ake samun raguwar masu fitowa su yi zabe a Nijeriya.
Ya ce, “Hukumar ta yi tunani sosai kan wannan al’amari. Shawarar da mu ka yanke ita ce akwai dalilai da yawa da su ka jawo raguwar masu kada kuri’a.
Dalilan Rashin Fitowar Masu Rajista Su Jefa Kuri’a:
“Daga cikin dalilan akwai rashin isasshen ilimantar da masu zabe da hakkokin su, da rashin ingancin gangamin jama’a, da tsoron barkewar rikici a lokacin zabe, sai rashin cika alkawarin da zababbun shugabanni su ka yi a lokacin takara, da kuma rashin yardar da jama’a ke yi wa hukumomin gwamnati.
“A yayin da Hukumar za ta ci gaba da yin aiki tare da kungiyoyi masu zaman kan su da ma dukkan masu ruwa da tsaki don tunkarar wadannan matsalolin, mun kuma yi amanna da cewar samun karin rumfunan zabe wani abu ne muhimmi wajen fitowar masu zabe a lokacin zabubbuka.
“Kasashe masu yawan mutane da ke fitowa domin kada kuri’a a lokacin zabubbuka kuma su na da isassun wuraren kada kuri’a cikin sauki da aka tanadar domin masu zabe da ke da rajista wadanda a kan yi wa sauyi lokaci-lokaci saboda karuwar yawan masu zabe. To amma abin bakin cikin shi ne mu ba haka abin ya ke ba a Nijeriya.”
Yakubu ya yi nuni da cewa Najeriya ta na da rumfunan zabe guda 119,973 wadanda aka samar a cikin 1996 a karkashin tsohuwar Hukumar Zabe ta Kasa, wato NECON, domin masu zabe da aka kiyasta yawan su ya kai miliyan 50.
“Har yanzu ba a kara yawan su ba a shekaru 25 da su ka gabata duk da yake yawan masu zabe da su ka yi rajista sun karu zuwa 84,004,084 ya zuwa 2019. Kuma yawan zai karu bayan mun ci gaba da yi wa sababbin masu zabe rajista saboda Babban Zaben 2023.”
Ya ce INEC ta yi nazarin dukkan kokarin da aka sha yi a baya da nufin fadada wuraren kada kuri’a, wato a kara rumfunan zabe, a shekarun 2007, 2014 da kuma kafin Babban Zaben 2019 da dalilin da ya hana a cimma nasarar hakan.
Yakubu ya ce hukumar ta gama fahimtar cewa akwai yiwuwar ba ta isar da burin ta ga sauran ‘yan Najeriya ba domin a samu shawarwarin su, don haka ba a fahimci abin ba har aka siyasantar da shi.
Ya ce zaman da INEC ta yi da wadannan kungiyoyi masu zaman kan su an yi shi ne a matsayin ci gaba da tuntubar da ake yi da dukkan masu ruwa da tsaki, tare da fatan ta hanyar yin hakan hukumar za ta fi isar da kudirin ta ga ‘yan Najeriya.
To amma ya yi kira ga kowa da kowa da ya kawo nasa shawarwarin domin a magance matsalar ba tare da bata lokaci ba da kuma fatan za a fito da hanyar da za a bi a rika yi wa tsarin kwaskwarima a nan gaba idan bukatar hakan ta taso.
Yakubu ya ce, “Na tabbatar da cewa ta hanyar yin aiki tare, za mu kafa tarihi wajen ganin a karshe mun magance wannan matsala da ta shafe shekara 25 ta bai wa masu zabe damar samun karin rumfunan zabe a Najeriya.