Gwamnati ta rufe asibitoci 103 a jihar Legas

0

Gwamnatin jihar Legas ta rufe asibitoci 103 a shekarar 2020 da aka kama suna aiki ba bisa tsarin dokar kiwon lafiya ba a jihar.

Shugaban hukumar HEFAMAA Abiola Idowu, ta sanar da haka a makon da ya gabata a birnin Ikko.

Abiola ta ce rashin ingantattun kayan aiki, rashin kwararrun ma’aikata, rashin yi wa asibitocin rajista sune dalilan da ya sa aka rufe asibitocin.

Ta ce yanzu dai gwamnati ta bude wasu daga cikin asibitocin bayan sun yi abin da ya kamata amma sauran za su ci gaba da zama a rufe har sai sun cika dokokin da aka saka.

Abiola ta yi kira ga mutane da su mara wa gwamnati baya ta hanyar tona asirin asibitocin dake aiki ba bisa doka ba.

A watan Disambar PREMIUM TIMES HAUSA 2020 ta buga labarin yadda gwamnati ta rufe manya da kananan shagunan siyar da magani 24 a fadin jihar.

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Akin Abayomi ya bayyana cewa an kama wadannan shaguna ne da laifukan da suka hada da saida magunguna a wuraren da basu da tsafta, bude shago ba tare da lasisi ba,siyar da magani ba tare da kwararren masanin magani ba kwantar da marasa lafiya tare da karin ruwa da sauran su.

Share.

game da Author