Hadimin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, Salihu Tanko ya ragargaji shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar sa ta APC a lokacin da ya rubuta cewa jam’iyyar sa, APC ta gaza, ta yaudari ‘Yan Najeriya ne rashin iya kawo karshen matsalar rashin tsaro da ame fama da shi a kasar.
Salihu ya ce ” Da ma fa talakawan Najeriya sun zabe mu ne domin a kawo musu karshen matsalar rashin tsaro da kasar ke fama dashi amma kuma maimakon sauki tabarbarewa da muni abin yayi.
” Ace wai a kullum aka tashi sai an kwashi mutane da sunan an yi garkuwa da su, abu kamar almara. Idan ba zaka iya ba ka hakura mana ka tattara ka yi tafiyar ka. Abin ya muni matuka.
Idan ba a manta ba, ranar Juma’a mahara suka kwashe daliban makarantar sakandare a Jangebe, jihar Zamfara.
Hakan kuma, har yanzu idan ba a manta ba, daliban makarantan Kagara na nan tsare a hannun masu bindiga ba a sako su ba.
Ba wannan bane karon farko da Salihu Tanko, ke ragargazar gwamnatin Buhari ba. A wancan lokaci gwamnan Kano Ganduje ya dakatar da shi da ga ci gaba da yi masa hidima, sai dai daga baya ya dawo da shi.
Discussion about this post