Kafin gwamnati ta karbi maganin rigakafin cutar korona hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta ƙasa NPHCDA za ta horas da jami’an lafiya 100,000.
Hukumar za ta horas da ma’aikatan ne domin samar da ma’aikatan lafiyan da za su rika yi wa mutane allurar rigakafin korona a kasar nan.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Mohammad Ohitoto ya sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Alhamis.
“Gwamnati ta fara horas da ma’aikatan lafiyan dake aiki da manyan asibitocin gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi su 13,000.
“Wadannan sune rukunin farko. Rukuni na biyu su ne ma’aikatan lafiya 100,000 dake aiki a asibitocin dake mazabun kasar nan da za a fara ranar 1 ga Maris.
Bayan haka gwamnati za ta bude wani shafi a yanar gizo domin mutane su yi rajistan yin allurar rigakafin.
“Yin rajistan ya shafi fadin rana da lokacin da mutum ke bukata a yi masa allurar rigakafin. Bayan an kammala mutum zai karbi lanba domin gabatar da shi a lokacin da za a yi masa allurar rigakafin.