Takaicin jidalin kasa karantu a fannin likitanci a jami’a ya sa ni kama harkar noma – Matashiya mai digirin fannin noma

0

Wata mace mai zuciyar neman na kan ta, mai suna Chinonye Ezom, kuma wadda ta kammala digiri a fannin kimiyyar kayan irin shukawa, ta shafe shekaru uku ta na noma.

Cikin 2014 ta yi kokarin shiga jami’a domin ta karanci ilmin sanin magunguna, wato Pharmacy, amma abin bai yiwu ba. Maimakon haka, sai ta samu aka ba ta kardar amincewa yin digiri a fannin nazarin kimiyyar sanin irin shukawa, wato Crop Science.

“Na ji haushi kuma na yi kuka, amma da na kira mahaifi na na shaida masa, sai ya ce ba komai, na karba kawai, na rumgumi kaddara. Kuma na hakura na karba din.”

Duk da haka Chinonye Ezem ba ta hakura ba, shekaru biyu a jere ta sake rubuta JAMB domin ta yi karatun digiri kan ilmin magunguna, amma makin da ake bukata ta samu bai kai ba.

A lokacin har ta shekara uku a jami’a, kuma ta fara sha’awar noma din ilmin amfanin gona da ta ke yi.

“Da na rubuta JAMB shekaru uku a jere ban samu makin da na ke so ba, sai na hakura da darasin da na keyi. A lokacin har na fara sabawa, kuma na fahimci ashe yadda na ke tunanin sa ya ma wuce nan.” Inji Chinonye.

Yanzu dai ta kammala digirin ta, kuma ta tsunduma cikin harkar noma, tun shekaru uku da su ka gabata.

Baya ga digirin da ta ke da shi, sai kuma ta garzaya ta yi wani aikin samun horon yadda ake kiwon dabbobi da inganta kayan gona a Songai Delta Farms ta garin Sapele.

“To ai bayan samun wannan horo da na yi, in gaya maka sai ido na ya kara budewa. Na gane ashe harkar noma ba wai a duka a yi ta kartar kasa ana noma ana gumi ke noman ba ma tukunna. Ashe ya wuce nan.” Inji ta.

Daga nan sai na je na yi tirenin a IITA, inda aka zabe mu mu shida a shirin bunkasa noman dankalin Turawa mai kalar launin lemun zaki.

Wato shi wannan kalar dankalin Turawa, ya na dauke da sinadarin Vitamin A mai kara lafiya. Masu ciwon suga na iya amfani da shi. Haka kananan yara za su iya cin sa domin kara lafiya.

“Sannan kuma ya na kare sinadaran garkuwar jikin dan Adam. Amma da ya ke babu wayar wa jama’a kai dangane da afamnin sa, to ya kamata ’yan Najeriya su san amfanin sa.”

Bankin Afrika na ADB ne ke daukar nauyin noma wannan dankali a wani gagarimin shirin TAAT ta hannun IITA da ake yi a Kogin Anambra Imo River Basin. Su ke bayar da fiin noma, su bayar da injinan noma kuma su bayar da kudin gudanar da noman da sauran irin shukawa da kayan da duk ake bukata.

“Baya ga wannan aiki da na ke yi da wadannan kungiyoyi na kasashen duniya, kuma ina aiki da Cibiyar Noman Dankalin Turawa ta Duniya” Inji Chinonye.

“Ni gona ta a jihar Imo ta ke. Kuma ban taba samun wata barazanar cinye min amfanin gona daga shanun makiyaya ba. Amma dai wasu abokai na sun fuskanci hakan.

“Nan da nan sai na dauki matakin yadda ba su ma iya sake shiga gona ta, ballantana su yi min barna.”

Sai dai kuma ta ce a lokacin da ta kwashe amfanin gonar ta, ribar da ta samu ba kai yadda ta yi tsammanin samu ba. Amma dai a yanzu ana kokarin gano yadda za a rika samun riba sosai.

Ta ce a matsayin ta na yarinya matashiya, gonar ta hekta daya ce kadai.

Sannan ta ce babu wata matsalar da su ke fuskanta wajen sayar da dankalin, domin kasuwa na bukatar sa sosai.

” Ko da yaushe akwai masu bukatar su saya. Wanda mu ke nomawa ma ba ya isar su. Har jira su ke yi a noma su biya nan take.”

Share.

game da Author