Babbar Daraktar Ofishin Kula da Basussuka na Najeriya, Patience Oniha, ta bayyana cewa jimillar tulin basussukan da kasar Chana ke bin Najeriya sun kai naira tiriliyan 3.2.
Oniha ta yi wannan bayani ne a cikin wata tattaunawar musamman da aka yi da ita, kuma PREMIUM TIMES na da rikodin din tattaunawar, wadda aka gabatar a ranar Labara.
Wannan tulin bashi da aka ciwo a Chana, ya kai kashi 11% bisa 100% na adadin yawan basusssukan da kasashen waje da cibiyoyin hada-hadar kudade na kasashen waje ke bin Najeriya bashi baki daya.
Sai dai kuma ta ce wannan tulin bashi da ya cika ruwan cikin Najeriya, baa bin damuwa ba ne matuka, saboda akwai wadanda yarjejeniyar zuba jari ce wajen gina wasu ayyukan raya kasa.
Irin wadannan yarjejeniya, ana kulla su ne tsakanin Najeriya da wani banki ko cibiya ko wata kasa. Misali, kamfanin da ya amince zai gina titin jirgin kasa, shi zai rika karbar kudaden shiga har sai ya karbe kudaden sa na aiki da ribar sa tukunna, sannan ya damka wa Najeriya alhakin karbar kudaden.
Oniha ta ce kafin bullar cutar korona cikin 2020, Gwamnatin Tarayya ta kudiri aniyar ciwo bashin naira tiriliyan 1.7 domin cike gibin kasafin kudin 2020. “To amma da korona ta addabi tattalinn arzikin mu da na duniya baki daya, sai aka kara gejin yawan bashin da za a ciwo domin cike gibin kasafin 2021 zuwa naira tiriliyan 4.2″
A cikin tattaunawar, Oniha ta nuna cewa ganin yadda Karfin Tattalin Arzikin Cikin Gida Najeriya (GDP) ya kasa wuce mizanin kaka-ni-ka-yi, to za a rika daga malejin ciwo bashi daga 25% bisa 100%, zuwa kashi 40% bisa 100% daga nan har 2023.