SHUGABANCIN WTO: Ngozi Okonjo-Iweala ta bayyana kudirorin ta

0

Tsohuwar Ministar Harkokin Kudade, wadda a yau ranar Litinin aka zaba shugabancin WTO, Ngozi Okonjo-Iweala ta bayyana kudirorin ta bayan tabbatar mata da shugabancin Kungiyar Hada-hadar Kasuwanci ta Duniya (WTO).

Ngozi ta yi wannan bayani jim kadan bayan zaben na ta da aka yi, wadda ita ce ‘yar Afrika ta farko da ta taba rike mukamin, kuma mace ta farko ac duniya da ta taba rike wannan kasaitacciyar kungiyar kasuwanci ta duniya.

Ngozi ta kara samun kwarin-gwiwar samun wannan babban matsayi bayan da a cikin makon da ya gabata kasar Amurka ta nuna goyon bayan ta ga tsohuwar ministar kudaden ta Najeriya.

Kafin nan dai Amurka a lokacin tsohon Shugaban Kasa Donald Trump, ta ki mara wa Ngozi baya kiri-kiri.

Ngozi wadda ta taba rike babban mukami a Bankin Duniya, ta kasance ba ta da aboki ko abokiyar takara, bayan da Ministar Cinikayyar Koriya ta Arewa, Yoo Myung-hee ta bayyana janyewar ta.

A ranar 1 Ga Maris za ta fara aiki a matsayin Babbar Daraktar Kungiyar Kasuwanci ta Duniya, yayin da wa’adin ta zai kare cikin 2025.

Sai dai kuma idan duniya ta gamsu da yadda ta gudanar da kungiyar wajen bunkasa tattalin arziki, to za a iya kara mata wasu shekaru biyar kuma.

Kwamitin mutum tara da su ka shafe watanni tara su na gaganiyar tantance ‘yan takara, sun taya Ngozi murna tare da yi mata fatan alheri cikin nasara.

Abin Da Zan Fi Maida Kai A Shugabancin WTO –Ngozi Okwonja-Iweala

Ngozi ta jaddada cewa za ta fi bada karfi sosai wajen ganin kasashen duniya da ke cikin wannan kungiya ta WTO sun shawo kan matsalar da annobar korona ta haifar wa tattalin arzikin duniya baki daya.

“Ina godiya da wannan karramawa da daukaka wacce aka kara min da aka zabe ni Shugabar Kungiyar Hada-hadar Kasuwanci ta Duniya (WTO).

“Idan aka kara wa Kungiyar WTO karfi sosai, to za ta kasance jagorar da za ta shige gaban sauran kasashen duniya domin ganin an maganance mummunar illar da cutar korona ta yi wa tattalin arzikin duniya.

“Wannan kungiya ta mu na fuskantar babban kalubale, amma ina da yakinin cewa idan mu ka hada karfi wuri daya, za mu iya kara karfafa kungiyar domin cimma kudirin bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya.”

Ngozi ta kafa babban tarihi a Najeriya, lokacin da ta ke Ministar Harkokin Kudade a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, inda ta shige gaba har aka yafe wa Najeriya dimbin bashin nan da aka ciwo daga kira Paris Club.

Share.

game da Author