Jigo a jam;iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya bayyana cewa a irin tangal-tangal din da jam’iyyar PDP ke yi yanzu ‘ya’yan jam’iyyar da dama za su canja sheka zuwa APC sai dai banda shi.
” Ni fa da kuke gani, da in fice daga PDP gara in koma un ci gaba da murza soyayya da matata abuna a gida.
” PDP ta yi min koma, tun ina shekara 42 na yi gwamna karkashin PDP, haka kuma duk abinda na yi, na samu a rayuwa, karkashin PDP ne. Saboda haka ina nan tare da ita kamar hanta da jini.
Maganar wai Femi Fani Kayode kuma karya ce.
” Ni da baki na, mun yi magana da shi ya karyata wannan magana, ya ce yana PDP ba zai kuma fice daga jam’iyyar ba.