Karancin Kororo Roba a Najeriya: Maimakon Roba biliyan 1.6 da ake bukata, milyan 500 kacal ake samu a kasar – Bincike

0

Sakamakon wani bincike da aka gudanar game da Kororo roba a Najeriya, ya nuna cewa ana bukatar akalla karin Kororo roba miliyan 564 duk shekara domin wadatar da mutanen kasar nan.

Hukumar NOIpolls, gidauniyar ‘AIDS HealthCare Foundation (AHF)’ da hukumar dakile yaduwar cutar kanjamau NACA suka gudanar da binciken sannan suka gabatar da sakamakon binciken ranar amfani da kororo roba a ranakun 13 da 14n Faburairu.

A taron wayar da kan mutane mahimmancin amfani da kororo roba a duk lokacin da za a yi jima’i jami’in shirye-shirye na gidauniyar AHF Taofeek Adeleye ya ce a lissafe dai mutanen Najeriya na bukatan kororo roba biliyan 1.15 amma sai dai kororo roba miliyan 587 ne ake da su a kasar nan.

Bayan haka shugaban hukumar NACA Gambo Aliyu ya ce baya ga wayar wa mutane kai hukumar ta gargadi masoya su rika yin amfani da kororo roba a duk lokacin da za a yi harka.

Aliyu ya ce mace ta rungumi namiji daya tilo ya fi mata akan ta rika tsalle-tsalle bata nan bata can sannan kuma ya na sa a kauce wa kamuwa da Kanjamau da wasu cututtukan da ake kamuwa da su a wajen jima’i.

Taron zai samar da hanyoyi da zai taimaka wajen inganta samar da kororo roba a ko una a fadin kasar nan batare da an samu matsala ba.

Share.

game da Author