RASHIN TSARO: Tsakanin mu da ’yan bindiga sai kwankwatsa, babu zancen Afuwa – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa “gwamnati za ta ci gaba da kwankwatsar masu hare-haren sunkuru, ’yan bindiga, masu garkuwa da sauran mabarnatan masu aikata laifuka.

Buhari ya ce babu maganar yi masu afuwa kwata-kwata, saboda haka tsakanin su da gwamnati sai dai a bi su kawai a dakile.

Ya ce gwamnati ba za ta tsaya ta na hawa teburin shawarar tattaunawa da mabarnata masu kashe mutane da yi wa rayuka barazana ba, ballantana har a yi masu afuwa.

Buhari ya yi wannan bayani a ranar Alhamis, wurin bude Taron Makomar Tsaron Arewacin Najeriya, wanda Gwamnonin Jihohin Arewa tare da Sarakunan Arewa su ka gudanar a Kaduna.

Jawabin na Buhari ya zo daidai lokacin da wasu shugabannin Arewa ke neman gwamnati ta yi wa tubabbun masu garkuwa da mutane afuwa.

Daga cikin wadanda ke neman a yi wa masu garkuwa da kisan jama’a afuwa, akwai Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara da kuma Sheikh Ahmad Gumi.

Haka nan akwai wasu ‘Yan Majalisar Tarayya su shida daga Zamfara da kuma Snatoci uku dukkan su na Zamfara, masu so a yi wa ‘yan bindiga afuwa kamar yadda aka yi wa ‘yan ta’addar Naje Delta.

Sai dai kuma a wurin taron na Kaduna, Buhari ya ce duk wani dan iskan mai laifin kashe mutane da garkuwa da fyade da satar dukiyar jama’a, to a matsayin mai laifi za a dauke shi, babu wata afuwa da za a yi masa.

Buhari wanda Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari ya wakilta, ya bayyana cewa barazanar da rashin tsaro ke haifarwa a kasar nan, ta hana ci gaba da kuwa kawo cikas ga fitar da talakawa daga kangin fatara, yunwa da kuncin rayuwa.

Buhari ya ci gaba da cewa tuni ya umarci shugabannin bangarorin tsaro su gaggauta fito da wanin tsarin da zai dakile duk wasu mabarnata a fadin sassa daban-daban na kasar nan.

Ya ce gwamnatin sa ba za ta taba saurara wa masu garkuwa da mutane ba da masu aikata duk wani nau’i na ta’addanci.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa “gwamnati za ta ci gaba da kwankwatsar masu hare-haren sunkuru, ‘yan bindiga, masu garkuwa da sauran mabarnatan masu aikata laifuka.

Buhari ya jinjina wa irin kokarin da Gwmnaonin Arewa su 19 da kuma sarakunan gargajiyar Arewa ke yi wajen ganin an shawo kan matsalar tsaro a Arewa.

Ya ce taron wanda aka shirya a Kaduna, ya zo daidai a lokacin da ya dace. Amma kuma a fitar da batun cewa Gwmnatin Tarayya ta yi afuwa ga masu garkuwa da masu aikata ta’addanci.

Share.

game da Author