Jim kadan bayan sako wasu daga cikin dalibai da malaman makarantan Kagara, mahara sun sake dirkakan garin Kagara in da suka kashe mutum hudu kuma suka yi garkuwa da wasu mutum 12.
Wani shugaban al’umma dake zaune ya Kagara ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa maharan sun sace mutum takwas a kauyen Kundu sannan wasu mutum 11 a kauyen Gunna dake karkashin Kagara, Karamar hukumar Rafi, Jihar Neja.
Ya kara da cewa mutum 4 da aka kashe suna kauyen Karako ne. Cikin wadanda aka tafi da su akwai limamin kauyen Madaka Malam Ibrahim Ruvo.
Tsohon shugaban Karamar hukumar Rafi, ya yi kira ga gwamnatin Jihar Neja su kara yawan jami’an tsaro a wannan yanki, domin abi fa ya wuce gona da iri.
Idan ba a manta ba da sanyin safiyar Asabar aka sako wasu daga cikin yaran makarantan Kimiyya dake Kagara da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su.