Wani mai wa’azin Kirista mai suna Bulus Yikura, ya yi rokon gaggawa ga gwamnatin Najeriya da kuma Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN), domin su tattauna yadda za su kubutar da shi daga hannun Boko Haram, ko kuma su kashe shi.
Cikin wani bidiyo fa aka nuno Yikura na magana cikin murya mai ban tausayi, ya ce wannan ce dama ta karshe da Boko Haram su ka ba shi ya yi magana, domin a tattauna yadda za a sake shi.
“Ina kira ga Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN), su gaggauta tattaunawa da wadanda ke rike da ni cikin sati daya. Domin wannan bidiyon shi ne dama ta ta karshe. Daga yau ba za a sake nuno ni ba. Idan ba a tattauna an ceci rayuwa ta ba, to bayan sati daya kashe ni za su yi.”
An nuno Yikura ya na magana da Hausa, a gaban wani dan Boko Haram wanda ke rike da zabgegiyar diga.
Yikura dai an kama shi a karshen watan Disamba, 2020, ranar Jabibirin Kirsimeti.
An kama shi a kauyen Pemi da ke kusa da Chibok, a wani hari da Boko Haram su ka kai kauyen, mai nisan kilomita 20 daga garin Chibok.
Ya ce shi mai aikin ibada ne a cocin EYN LCC, kuma idan ba a ceto shi ba zuwa ranar 4 Ga Maris, to kashe shi za a yi.
A karshe ya nemi a taya shi addu’a Ubangiji ya kubutar da shi.
An nuno wanda ke tsaye a gaban sa, ya na cewa idan ba a zo an tattauna karbar sa ba, to za su kashe shi.
Discussion about this post