KORONA: Mutum 1,368 sun kamu, 16 sun mutu a Najeriya ranar Talata

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,368 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata. Sannan kuma mutum 16 suka rasu a dalilin Korona a wannan rana.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa jihar Anambra ta samu karin mutum -344, Oyo-172, FCT-148, Benue-107, Rivers-95, Ogun-59, Ondo-56, Ebonyi-53, Kaduna-52, Filato-46, Kwara-36, Enugu-30, Akwa Ibom-26, Osun-22, Edo-20, Abia-17, Kano-16, Borno-15, Cross River-10, Delta-8, Gombe-8, Imo-7, Ekiti-5, Sokoto-4, Jigawa-3, Bayelsa-3, Nasarawa-3 da Zamfara-3.

Yanzu mutum 148,296 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 124,483 sun warke, 1,777 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 22,036 ke dauke da cutar a Najeriya.

Ranar Litini, mutum 574 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Edo, Ondo, Kwara, Kano, Ogun da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –53,292, FCT–18,741, Filato –8,737, Kaduna–8,158, Oyo–6,498, Rivers–6,098, Edo–4,323, Ogun–3,805, Kano–3,536, Delta–2,489, Ondo–2,824, Katsina–2,017, Enugu–1,954, Kwara–2,675, Gombe–1,951, Nasarawa–2,123, Ebonyi–1,754, Osun–2,190, Abia–1,355, Bauchi–1,207, Borno-1,202, Imo–1,358, Sokoto – 767, Benue-1,162, Akwa Ibom–1,294, Bayelsa 722, Niger–895, Adamawa–725, Anambra–1,615, Ekiti–702, Jigawa 492, Taraba 584, Kebbi 306, Yobe-260, Cross River–242, Zamfara 218, Kogi–5.

Shugaban hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa mutum 29 sun kamu da sabuwar nau’in cutar korona mai suna ‘B117’ a Najeriya.

Ya ce an gano wadannan mutane a jihohin Edo, Kwara, Lagos, Osun, Oyo da babban birnin tarayya Abuja.

Ihekweazu ya ce masana kuma likitoci masu bincike a cibiyar ACEGID na jami’ar Redeemers dake jihar Osun ne suka gano cutar a jikin wadannan mutane.

Ya ce ga dukan alamu cutar ta yadu a kasar nan a dalilin haka likitocin za su ci gaba da budanar da bincike domin gano sauran mutanen da suka kamu da cutar.

Share.

game da Author