A yanzu di ba sabon labari ba ne cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa sunan Abdulrasheed Bawa, a matsayin wanda ya ke so ya maye gurbin korarren Shugaban EFCC, Ibrahim Magu.
Labarin shi ne, wanda aka nada din a yanzu, dan asalin Jihar Kebbi ne, Jihar da Ministan Shari’a Abubakar Malami ya fito.
Dama kuma shi shugaban EFCC tamkar ya na karkashin Ministan Shari’a ne, ba ya gurfanar da gagga da kananan barayin gwamnati sai da shawarar Ministan Shari’a, wanda shi ne Antoni Janar na Tarayyar Najeriya.
Sannan kuma Malami ne ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari wasikar korafin zargin cewa Magu na cuwa-cuwa, har ta kai aka damke shi a cikin watan Juli, 2020.
Bayan ya yi kwanaki a tsare, aka sake shi, amma kuma ana kafa masa kwamitin bincike, a karkashin tsohon Cif Jojin Najeriya, Ayo Salami.
Watanni hudu bayan kammala bincike, har yau ba a fito an bayyana tantagaryar laifin da Magu ya yi ba. sannan kuma a asirce a ka yi zaman sauraren binciken na sa.
PREMIUM TIMES HAUSA ta rika buga laifin zarge-zargen da aka yi wa Magu, ciki har da mallakar kadarori a Dubai.
Sai dai a lokacin da Magu ke karyata zarge-zargen da aka yi masa, shi ma ya zargi ogan sa, Minista Malami da kulle-kullen hada baki da wadanda ake zargi da da sayar da kadarorin da aka kwace a hannun manyan barayi a hanyar da ba ta dace ba.
Sannan kuma ya zargi Malami da hana-ruwa-gudu wajen tadiye wasu bincike da kuma kokarin maido tsohuwar Minsitar Harkokin Man Fetur, Diezani Allison-Maduekwe gida Najeriya, domin a tuhume ta, a hukunta ta.
Wane Ne Bawa, Sabon Shugaban EFCC
Abdulrasheed Bawa dai Mataimakin Sufurtandan Binciken Kwakwaf ne a ofishin EFCC.
An nada Bawa shugabancin masu binciken tsohuwar Ministan Harkokin Man Fetur, Diezani Alison-Madueke a cikin 2015, ita da abokan harkallar ta.
Har zuwa ranar Talata da aka bayyana sunan sa a matsayin sabon shugaban EFCC, shi ne ke shugabancin bangaren binciken Diezani.
Idan dai har Majalisar Dattawa ta amince da nadin da Buhari ya yi masa, zai kasance mafi karancin shekaru a cikin wadanda su ka taba yin shugabancin Hukumar EFCC.
Tun daga 2015 har yau dai EFCC ba ta da tsayayen shugaba. Magu ya shafe shekaru ya na riko. Kuma har ya sauka ba a amince da shugabancin sa ba a Majalisar Dattawa. Haka shi ma wanda ke kai a yanzu, riko ya ke yi.
Shekarun Abdulrasheed Bawa 40 a duniya. Nuhu Ribadu da ya hau shugabancin a cikin 2003 zuwa 2007, ya kama shugabancin ya na da shekaru 43 ne.
Banda karancin shekarun da ya ke da shi, idan Majalisar Dattawa ta amince da Bawa, zai kasance mutum na farko da ya fara shugabancin EFCC ba tare da ya taba yin aikin dan sanda ba.
Dama kwamitin Ayo Salami ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari a cikin shekarar da ta gabata cewa a rika nada wand aba a cikin ‘yan sanda kadai zai fito ba.
Har yau dai ba a taba nada wanda ba dan Arewa a shugabancin EFCC ba.
Bawa dai dan asalin Jihar Kebbi, ne jihar su daya da Ministan Shari’a Abubakar Malami, wanda ya yi sanadiyyar sallamar Magu daga aiki.
Ya yi digirin san a farko da na biyu a Jami’ar Usman Danfodiyo, Sokoto.
Ya shiga aikin EFCC a matsayin Mataimakin Sufeton Binciken Kwakwaf (ADS) cikin 2004.
Digirin san a farko a fannin tsimi da tanadi ya yi shi. Nabiyu kuma a kan Huldar Diflomasiyya ya yi.
Bawa ya shafe shekaru 15 ya na aiki a EFCC, a halin yanzu ya na karatun digiri na shari’a a Jami’ar London.
Kuma har zuwa yau shi ne shugaban EFCC Shiyyar Lagos.
Ya yi aiki a wurare da dama, kuma ya binciki manyan barayin gwamnati da harkallolin kudade masu dimbin yawa da binciken barayin danyen mai.
Bawa: Bawan EFCC Ko Bawan Malami?:
Tilas nada Abdulrasheed Bawa ya haifar da cece-ku-ce a kasar nan, ganin cewa jihar su daya da ogan sa, Ministan Shari’a Abubakar Malami.
Sannan kuma Malami ne sanadiyyar korar wanda aka sauke, Ibrahim Magu bayan sun samu sabani da rashin jituwa a tsakanin su. Har Malami ya rubuta takardar korafi kan Magu ga Shugaba Buhari.
Wannan takarda ta yi sanadiyyar kamawa, kullewa, bincike da korar Magu.
To amma kuma nada dan jiha daya da Malami, zai iya kawo shakku a zukatan jama’a, ko da kuwa babu wani abin da za a yi wa shakku a lamarin.
Yanzu dai ya rage mu ga cewa shin Bawan da Buhari ya nada, bawan EFCC ne ko kuwa bawan Malami zai zama.
Lokaci shi ne alkali kuma shi ne mizani da ma’auni.
Discussion about this post