Kotu dake Igando jihar Legas ta warware auren shakara 15 dake tsakanin Shehu Isa da Amina saboda rashin jituwa da maida matarsa jaka da yayi.
Alkalin kotun Adeniyi Koledoye ya warware auren ranar Litini saboda mijin Amina wato Shehu ya ki bayyana a gaban Kotun.
Alkalin ya baiwa Amina ‘ya’yan su biyu da suka haifa ta ci gaba da rike su.
Uwargidan Isa, Amina ta shaida wa Kotu cewa tsananin duka da take sha wajen mijinta kawai ya isa su rabu domin ya maida ta yadda kasan jaka.
” Ni fa har fargaba nike yi kada fa a irin dukan da Isa yake yi min kullum ya yi sanadiyyar rayuwata. Karamin abu idan ya bata masa rai sai kawai ya hau ni da duka, duka kuma ba na wasa ba.
” Haka kuma idan muka samu sabani a wajen saduwa irin ta aure sai ya hau ni da duka, sannan idan na yi barci can anjima sai ya kamfato ruwan sanyi a bokiti ya kwarara min.
Amina ta ce wadannan ne dalilan da ya sa take rokon kotu ta raba auren ta da Isah tana mai cewa ta gaji da zaman ukuba da take yi.
Shi ko mijin Amina, wato Isa, yaki bayyana a Kotu ko da aka kai masa sammaci.