Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefile, ya bayyana cewa Matatar Man Fetur ta Dangote za ta rika sayar a albarkatun man da za ta rika tacewa a farashin naira, a nan cikin gida Najeriya.
Emefile ya yi wannan jawabi a ranar Asabar, lokacin da ya kai ziyarar ganin yadda aikin kafa Matatar Dangote ke tafiya a Lagos.
Emefele ya kai ziyarar ce a bangaren da za a rika tace danyen mai ana sarrafa takin zamani sai kuma bangaren binne bututun mai da ake aikin yi Ibeju Lekki, Lagos.
Gwamnan na Babban Bankin Najeriya ya ce matatar Dangote za ta fara sayar da takin Urea a cikin watan Maris, domin bunkasa harkokin noma a kasar nan.
Emefile ya yi nuni da cewa masana’antar Dangote wadda za a kashe dala bilyan 15 wajen kammala ta, za ta ceto Najeriya daga kashe kashi 41 bisa 100 na kudaden musayar kasashen waje shigo da dangogin man fetur da sauran su.
“Bisa yarjejeniyar da kamfanin NNPC ya yi da kamfanonin mai, Matatar Dangote za ta iya sayen danyen mai a farashin naira, ta tace shi sannan ta rika sayarwa a Najeriya a farashin naira.”
Ya ci gaba da bayyana cewa wannan hada-hada za a rika yi da Matatar Dangote za ta kara sa nau’o’in kayayyakin da ake sarrafawa daga danyen man fetur su kara sauki, arha takyaf a Najeriya.
“Idan mu ka samu sa’a da nasara, Masana’antar Dangote za ta rika sarrafa kayayyakin da sun fi karfin amfanin iyar cikin Najeriya kadai. To kun ga daga nan kuma sai masu hada-hadar kasuwanci a Najeriya su rika sayen lodin kananan jiragen ruwa na kayan Dangote ana fitarwa zuwa cikin kasashen Afrika ta Yamma ana sayarwa a farashin naira.”
Gwamnan CBN ya ce ya na da yakinin za a iya kammala aikin kafa Matatar Dangote daga nan zuwa cikin shekarar 2022 can wajen tsakiyar shekarar.