Fitaccen dan Najeriya Wole Soyinka, ya nuna matukar bacin rai dangane yadda ake yawan kama mutane kamar tsuntaye ana garkuwa da su.
Ya ce idan ‘yan Najeriya ba su tashi tsaye ba, to fa za a wayi gari ba tashi duk wani wani mai karafin karfi an damke shi an yi garkuwa da shi.
Dangane da munin lamarin ne Soyinka ya ce ya na goyon bayan daga yau ko kutum daya aka kara kamawa a wata jiha, to shawaarar sa ita ce gaba daya al’ummar jihar su fito su yi fashin zuwa aiki. A tsaida komai cak, kuma sauran jihohi ma su mara wa jihar baya.
Da ya ke magana a wurin wani taron da Kungiyar Marubuta ta ANA ta shirya a Abeoukuta, babban birnin Jihar Ogun, Soyinka ya nuna bacin ran yadda kiri-kiri gwamnati ta yi sakacin da har garkuwa da mutane na neman zama wata al’ada ko dabi’a a kasar nan, musamman a Arewa.
Ko a cikin watan Disamba, Soyinka ya bayyana cewa zai yi wuya mai hankali ya yarda cewa akwai mai rike da akalar Najeriya a yanzu.
Fitaccen mai fada a ji Wole Soyinya, ya bayyana cewa zai yi wahala a tunkari mai hankali a ce masa akwai mai rike da akalar Najeriya a halin yanzu, kuma har ya yarda.
Soyinka ya ce a gaskiya Najeriya ba ta da shugabanni masu hangen nesa kwata-kwata.
Ya yi wannan bayani ranar Laraba, lokacin da ya ke magana kan kalubalen da Najeriya ta fuskanta cikin 2020.
Ya ce shekarar 2020 ita ce shekarar da ya yanke kauna kan lamuran gyaran kasar nan, saboda babu shugabanni masu hangen nesan da za su iya tsamo ta daga dagwalon da su ka jefa ta, har su yi mata wankan sake tsaftace ta.
Ya yi bayanin a Ibadan, wurin kaddamar da littafin sa mai suna, “The chronicles of the happiest people on earth”, wato ” Jadawalin mutanen da su ka fi rayuwar farin ciki a duniya.
Soyinka ya ce ya shafe shekaru 40 cur ya na tattara bayanan da ke cikin littafin mai shafuka sama da 500.
“Irin yadda shekarar 2020 ta zo sabubba marasa dadi da dama, kuma ga shi har shekarar ta zo karshe, amma har yanzu mun kasa hudu, sai tuma tsalle kawai mu ke yi wuri daya.
“Ba na so a ga kamar ina ta kiran jafa’i, amma dai ni wannan shekara ce na fi yanke kauna kan Najeriya. Ba wai don saboda barkewar korona ba. Masifu da bala’o’i sun faru, kuma har yanzu ha shekarar ta zo karshe, amma agiya na jike, an kasa daure kaya.”
“Shin masifun nan sun faru ne saboda kaddara ko kuwa dalilin sakacin wadanda ke ganin kamar alfarma su ke wa matane don su na shugabantar su?
“Gaskiyar magana ba haka ya kamata kasa ta ci gaba da wanzuwa ba. Na haka ya kamata dan Adam ya ci gaba da rayuwa ba. Yanzu abin ya kai makurar da idan ka fita, ba ka ma san inda za ka ba. Kuma ba ka ma san iyar inda za ka yada zango ba.”
“Kamar yadda na sha fada a baya, yanzu ma ina kara fadi, an kai munzilin da wahala mutum ya yarda cewa akwai masu jan akalar Najeriya a yanzu.”