RIKICIN SARAUTAR BILLIRI: Gwamna Inuwa ya gargadi masu tada fitina su rungumi zaman lafiya ko su kuka da kan su

0

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya gargadi masu tada fitina a garin Billiri su shiga taitayinsu tun da wuri ko kuma su yaba wa aya zaki.

Gwamna Inuwa yayi wannan gargadi ne a taron sarakuna da masu fada aji a jihar, inda ya nuna rashin jin dadin gwamnati na irin asarar da aka tafka saboda nadin sarautar sabon sarki.

” Kafin a yi kokarin nada sabon sarki a Billiri, wanda ba ma musulmi ko kirista ba ya taba yin sarki a garin, wanda ya rasu Kirista ne, yanzu kuma kawai sai wasu su hayayyako su ce ba za a nada wani sai wanda suke so.

” Ina gargadin mutanen yanki cewa gwamnati ba za ta zuba ido ta bari wasu na daukar doka a hannun su ba. Kawai don rigima ra barke sai su tare hanyoyin gwamnatin tarayya suka tare matafiya da basu ji ba basu gani ba haka ka kawai. Hanyar su ne, ko kuma su suka gina hanyar?

Bayan haka ya hori mazauna wannan gari da su koma su yi karatun ta natsu domin gwamnati ba za ta bari wani abu mai kama da haka ya sake faruwa ba.

” An kona kasuwanni, shaguna, wuraren ibada sannan an kashe mutane. Ina amfanin haka, tsakani da Allah, kawai saboda wai sarauta. Wadanda ba su ji ba ba su gani an halaka su. Kuma ma wannan sarauta duk gida daya ne. Kawai banbancin addini ne ya raba, kuma da can musulmi ne yayi aka baiwa Kirista, yanzu kuma kirista ya rasu shi kenan sai a shigo da siyasa a raba kan mutane.

A karshe gwamnan yayi kira da a zauna lafiya a tsakanin juna kuma masu son ta da zaune tsaye kuma ” Muna ji kuma muna gani za mu dandana kudar su domin basu fi karfin gwamnati ba.

Share.

game da Author