Fitaccen dan Najeriya Wole Soyinka ya bayyana cewa ya na goyon bayan Bishop na Sokoto, Matthew Kukah dangane da sakon sa na Sabuwar Shekara.
Soyinka ya ce irin martanin da aka rika maida wa Kukah an yi ne kawai don a karkatar da hankulan jama’a daga wani ab, kuma ba abin alheri ba ne ga zamantakewar al’umma a cikin kasa.
Dattijo Soyinka ya gargadi ‘yan Najeriya kada su sake borin wasu masu karya da addini a kasar nan ya yi tasiri a kan su.
Ya ce batun a tsaya har ana ja-in-ja kan maganar Kukah, da yarda da shi da kin yarda da shi duk bai ma taso har a tsaya ana jayayya ba.
Ya ce batun a tsuguna gefe ana yi wa jawabin Kukah fassara da fahimtar addini ko lullube bayanan na sa da rigar addini, abu ne da ya karkatar da jama’a daga ainihin damuwar da Kukah ya ce ke zukatan jama’a.
Soyinka ya nuna damuwa da yadda aka rika yi wa bayanan Kukah gurguwar fassara da fahimta, a daidai lokacin da kasar Amurka ta nemi fadawa irin halin da masu ruguguwar fahimtar addini su ka meni maida zaben Amurka batun addinanci.
Daga nan ya ce ba ma ragargazar da wani bangaren Musulmi su ka rika yi wa Kukah har su na ganin laifin sa ne abun damuwa ba.
“Yadda wasu kungiyoyi su ka yi masa barazana har su ka neman su fitar da shi daga mazaunin sa shi ne mafi damuwa.”
Soyinka ya ce duk wata al’ummar da ta san tasirin zamantakewar mabambantan jama’a a wuri daya, ba za ta yi maraba da masu yi wa Kukah barazana ba.
“Ni dai na bibiyi jawabin Kukah Dalla-dalla, amma ban ga wani ko da wuri daya ba da ya ci zarafin addinin musulunci. Amma fa ban ce na fi kowa sanin addini a duniya ba.”
Daga nan sai ya tunatar cewa a baya Gwamna El-Rufai ya sha ragargaza saboda zargin ya ci zarafin Isa Almasihu.
“To amma bi da na yi nazari, sai na ga babu wani sabon abu da El-Rufai ya fada. Kawai dai jirwaye ne ya yi mai kama da wanka.”
Amma sai aka samu masu kiran kan su Zaratan Sojojin Kirista (Onward Christian Soldiers) karkashin CAN, su ka nemi El-Rufai ya janye kalaman da ya yi.
Ya kara da cewa su fa masu zafafawa kan ra’ayin fahimtar addini ko da babu wannan batu a cikin mas’ala, idan su ka matso ka ka gusa baya da inci daya. To gaba kuma so su ke yi idan sun matso ya gusa da tazarar mil daya.
Soyinka ya nuna damuwa kannyadda jama’a kadan su ke jira sai su fito da wata fahimta ta daban.
Musamman ya yi magana kan wadanda su ka jefo maganar addini cikin ‘BLACK FRIDAY’.