Duk da matsin tattalin arzikin da Najeriya ta rufta a cikin 2020, amma Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa saurin damka wa Shugaba Muhammadu Buhari Kasafin 2020 cikin lokaci ya inganta tattalin arzikin kasar nan.
Da a ce ba a mika kasafin kudin 2020 cikin watan Disamba ba, to da matsin tattalin arzki da koma-bayan da za a fuskanta a kasar nan, sai ya yi muni fiye da yadda aka fuskanta sosai a 2020 din.
Cikin watan Nuwamba, 2020 ne tattalin arzikin Najeriya ya kara durkushewa a karo na biyu a lokacin ne alkadarin tattalin arzikin da ake riritawa a cikin gida ya karye tsawon watanni shida cur.
Magori Wasa Kan Ka Da Kan Ka:
Yayin da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawal ke wa manema labarai bayani domin murnar cikar haihuwar sa shekaru 62, ya bayyana cewa matsin tattalin arzikin da ka shiga cikin 2020 bai yi muni sosai ba, domin Majalisa ta yi gaggawar sakin kasafin kudi. Ba don haka ba inji shi, da ‘yan Najeriya sun ci kwakwa fiye da wadda su ka ci a 2020 din.
“Masana sun shaida mana cewa matsin tattalin arziki zai ragu a samu waraka sosai a karshen watan Maris mai zuwa.
Daga nan ya ce ba da dadewa ba za su yi nasarar sakin kudirin dokar man fetur a cikin shekarar 2020.
Ya ce duk masu nemn yi wa kudirin dokar kafar-ungulu ba za su yi nasara ba.
Ya ce majalisa za za ta yi bakin kokari ta taka wa duk masu neman ganin bayan kudirin burki.
Sai dai kuma Lawan bai fadi sunayen masu neman yi wa kudirin dokar kafar-ungulu ba.